Shugaba Tinubu Ya Rada Wa Babbar Jami'a a Najeriya Sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi
- Bola Ahmed Tinubu ya canza sunan jami'ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare zuwa Jami'ar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
- Shugaban kasa ya rada wa jami'ar sunan marigayin ne domin karrama shi saboda irin gudummuwar da ya bayar wajen hadin kai da gina kasa
- Tinubu ya fadi haka ne yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya gidan Sheikh Dahiru Bauchi yau Asabar, 20 ga watan Disamba, 2025
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi, Nigeria - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya karrama marigayi jagoran darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi yayin da ya kai wa iyalansa ziyarar ta'aziyya har gida.
A yau Asabar, 20 ga watan Disamba, 2025, Shugaba Tinubu ya ziyarci gidan marigayi Sheikh Dahiru Bauchi domin yi wa iyalansa ta'aziyyar wannan babban rashi da suka yi.

Source: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa yayin wannan ziyara, Shugaba Tinubu ya karrama marigayin ta hanyar canza sunan Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare, Jihar Bauchi.
Tinubu ya sa wa jami'a sunan Dahiru Bauchi
Mai girma shugaban kasa ya sanar da canza sunan jami'ar zuwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi University of Health Sciences, Azare, a jihar Bauchi.
Shugaban Ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da ya kai ziyara ta jaje ga iyalai da mabiyan marigayin malamin a birnin Bauchi.
A jawabin da ya gabatar, Shugaba Tinubu ya yaba matuƙa da rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi, inda ya bayyana shi a matsayin babban malami nagari, kuma jagoran tarbiyya.
Abin da Tinubu ya fada kan Dahiru Bauchi
Ya ce Sheikh Dahiru Bauchi mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen bauta wa Allah, hidimar al’umma da kuma gina ƙasa.
Ya ce koyarwar marigayi Sheikh Dahiru Bauchi kan gaskiya, riƙon amana da kyawawan ɗabi’u sun yi tasiri sosai ga al’ummomi da dama a faɗin Najeriya, tare da zama abin koyi ga kowa.

Source: Facebook
Tun farko dai jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa Shugaba Tinubu ya isa Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 4:50 na yamma.

Kara karanta wannan
An sanya dokoki a gari saboda ziyarar da Bola Tinubu zai kai gidan Sheikh Dahiru Bauchi
Yadda aka tarbi Tinubu a Bauchi
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya tarbe shi tare da Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ministoci da manyan jami’an gwamnati.
Daga cikin ministocin da suka je tarbar akwai Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, da kuma Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, tare da wasu jiga-jigai.
Haka kuma, wasu daga cikin tawagar Shugaban Ƙasar sun haɗa da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da sauran manyan jami’an gwamnati.
An tsaurara matakan tsaro a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Bala Mohammed ta rufe wasu hanyoyi tare da sauya akalar wasu a birnin Bauchi saboda ziyarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mai magana da yawun gwamnan Bauchi ya bukaci jama'a su bai wa jami'an tsaro hadin kai domin tabbatar da komai ya tafi cikin kwanciyar hankali.
Hadimin Gwamna Bala ya bayyana cewa matakin ya zama dole ne domin kare lafiyar jama’a da kuma tabbatar da ziyarar Shugaban Ƙasa ta gudana cikin lumana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
