Zamfara: Shaidanin Dan Bindiga, Isihu Buzu Ya Halaka bayan Guntule Masa Kai
- ’Yan sa-kai da jami'an Civilian Joint Task Force (CJTF) sun tabbatar da hallaka shahararren jagoran ’yan bindiga
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa an aika hatsabibi, Kachalla Isihu Buzu lahira a wani samame a Zamfara
- An ce Buzu ya shahara wajen kai hare-hare, garkuwa da mutane da razana al’ummomi a Zamfara da jihohin makwabta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Mambobin Civilian Joint Task Force (CJTF) sun tabbatar da kashe shahararren jagoran ’yan bindiga, Kachalla Isihu Buzu.
An tabbatar da mutuwar shedanin ne a wani gagarumin samame da aka gudanar a jihar Zamfara, abin da ke nuna ci gaba a yunkurin dakile ta'addanci.

Source: Original
Hatsabibin dan bindiga ya mutu a Zamfara
Rahoton Bakatsine da ke kawo bayanai game da tsaro ya tabbatar da haka a yammacin yau Asabar 20 ga watan Disambar 2025 a shafin X.
A cewar majiyoyin tsaro, an kaddamar da farmakin ne bayan samun sahihin bayanan sirri kan maboyar wannan jagoran ’yan bindiga.
An ce an dade ana alakanta shi da jerin hare-haren ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma kai farmaki ga al’ummomin karkara a Zamfara da wasu jihohin da ke makwabtaka da ita.
Rahotanni sun ce ’yan CJTF sun yi arangama mai tsanani da Buzu da mambobin tawagarsa, inda aka kashe shi a fafatawar, lamarin da ya haddasa tarwatsewar sauran ’yan bindigar da ke tare da shi.

Source: Original
Barnar da Kachalla Buzu ya yi a Zamfara
Mazauna al’ummomin da abin ya shafa sun bayyana wannan nasara a matsayin samun sauƙi, suna cewa Kachalla Isihu Buzu ya shafe shekaru yana razana jama’a ta hanyar kai hare-hare kan ƙauyuka, gonaki da manyan hanyoyi.
Shugabannin al’umma sun ce ayyukan Buzu sun haddasa lalacewar tsarin rayuwa, tilasta wa jama’a barin muhallansu, tare da tabarbarewar tsaro.
Duk da cewa har yanzu ana jiran sanarwa a hukumance daga jami’an tsaron gwamnati, CJTF ta jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da jami’an tsaro na hukuma domin kare al’umma.
Masu nazarin sun kuma jaddada buƙatar samar da manyan tsare-tsare da suka haɗa da dakile yaduwar makamai, inganta musayar bayanan sirri, da magance matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da ke haddasa rashin tsaro.
Gwamnatin Jihar Zamfara ta sha alwashin ci gaba da ba da goyon baya ga ingantattun shirye-shiryen tsaron al’umma da doka ta amince da su, yayin da mazauna yankin ke kira ga ƙara kaimi wajen gudanar da ayyukan tsaro domin kawar da sauran ragowar ’yan bindiga da dawo da zaman lafiya gaba ɗaya.
'Yan bindiga sun hargitsa gari a Zamfara
Mun ba ku labarin cewa wasu 'yan bindiga sun bi dare inda suka kai mummunan hari a kan mazauna kauyen Zamfara suna tsaka da barci.
Harin ya faru da tsakar dare a karamar hukumar Bungudu, lamarin da ya samu jama'a babu zato ko tsammani tare da asarar rai.
Jami’an tsaro sun fara farautar masu laifin domin ceto wadanda aka sace yayin da jama'a ke ci gaba da zama cikin zulumi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

