Kano da Borno Sun Yi Zarra yayin da Aka Sanar da Sakamakon Gasar Karatun Kur'ani Ta Kasa
- An kammala gasar karatun Alkur'ani ta kasa karo na 40 a tarihi, wanda ya gudana a Maiduguri, babban birnin jihar Borno
- Gwamna Babagana Umaru Zulumu ya bayyana cewa karbar bakuncin gasar da Borno ta yi na nuna cewa jihar ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali
- Borno da Kano ne suka lashe gasar bangaren mata da na maza kamar yadda sakamakon da aka sanar ya bayyana
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno, Nigeria - Rahotanni daga jihar Borno sun tabbatar da cewa an kammala gasar karatun Alkur'ani ta kasa wacce aka gudanar a Maiduguri.
Jihohin Kano da Borno ne suka samu nasarar zama zakarun bana 2025 a bangaren mata da bangaren mata a gasar, wacce ta kunshi wakilai daga jihohi 30 a fadin Najeriya.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Borno da Kano sun zama zakarun gasar Karatun Alƙur’ani ta Ƙasa ta bana, inda Borno ta lashe rukunin maza, yayin da Kano ta yi nasara a rukunin mata.
Kano da Borno sun zama zakarun 2025
Shugaban Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci a Jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto, Farfesa Abubakar Yelwa, shi ne ya sanar da sakamakon gasar gaba daya
Ya ayyana Musa Ahmed Musa daga Borno a matsayin zakaran rukunin maza, yayin da Hafsat Muhammad Sada daga Jihar Kano ta lashe kambun a bangaren mata.
Gasar, wacce ita ce ta 40 a tarihin gasar karatun Alkur'ani ta Najeriya, ta ɗauki tsawon mako guda, inda hafizai 296 daga jihohi 30 suka fafata a rukuni shida daban-daban.
Gwamna Zulum ya yi jawabi a wurin
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa nasarar karɓar baƙuncin gasar ta shekarar 2025 alama ce ta dawowar zaman lafiya a jihar Borno.
Ya ce gasar ta nuna jajircewar al’ummar Borno wajen neman zaman lafiya, ilimi da kuma koyon addini, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito
Zulum ya ce:
“Karɓar baƙuncin wannan gasa ta 40 ba kawai ɗaukaka ba ce ga Jihar Borno, alama ce mai ƙarfi ta jajircewarmu wajen tabbatar da zaman lafiya, ilimi da karatun Alƙur’ani mai girma.
“Jihar Borno na ci gaba da kokarin sake gina kanta, tabbatar da zaman lafiya da bai wa ilimi, na zamani da na addini, muhimmanci.
"Gudanar da wannan gasa ta ƙasa cikin nasara saƙo ne ga duniya cewa: Borno ta dawo, Borno ta samu zaman lafiya, kuma Borno cibiyar ilimi da tarbiyya ce.”

Source: Facebook
Gwamnan ya taya zakarun gasar da dukkan mahalarta murna, yana mai cewa nasararsu ba kawai cin gasa ba ce, illa sakamakon jajircewa, ladabi da girmama kalmar Allah.
“Duk wanda ya tsaya ya karanta Alƙur’ani a gaban alƙalai, zakara ne. Ainihin manufar gasar ba kyauta kaɗai ba ce, illa neman ilimi da ƙarfafa guiwar matasa," in ji Zulum.
'Dan Najeriya ya zo na 3 a gasar duniya
A wani labarin, kun ji cewa dan Najeriya, Buhari Sanusi daga Kano, ya zo na uku a gasar Alƙur’ani ta duniya da aka gudanar a Masallaci mai alfarma a Saudiyya.

Kara karanta wannan
Ba a gama murnar cin zabe ba, yan ta'adda sun sace mataimakin ciyaman da kansiloli 2
Rahotanni sun nuna cewa Buhari Sanusi ya zo na uku cikin mahalarta daga ƙasashe 128 daga kaashen duniya da suka fafata a gasar.
Nasarar ta sanya Najeriya cikin farin ciki da alfahari, musamman ganin cewa sauran matasan Musulmi daga Tchadi da Saudiyya suka rike matsayi na farko da na biyu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

