Dubu Ta Cika: DSS Ta Gurfanar da Wanda Aka Kama da Hannu a Kisan Masu Ibada 19
- Hukumar DSS ta maka Abdulmalik Abdulazeez Obadaki a gaban kotu bisa zargin hannu a harin da aka kai wata coci a jihar Kogi
- Ana zargin dai Obadaki ne ya jagoranci kai harin tare da hallaka mutane akalla 19 suna cikin ibada a wani coci a shekarar 2012
- Bayan gurfanar da shi, wanda ake zargin ya musanta galibin tuhume-tuhumen da ake masa, ya ce laifi daya ya san ya aikata
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kogi, Nigeria - Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Ƙasa (DSS) ta gurfanar da wanda ake zargin da kitsawa tare da jagorantar kai hari wata coci, tare da kashe masu ibada a jihar Kogi.
Mutumin mai suna Abdulmalik Abdulazeez Obadaki, ana zarginsa da jagorantar harin da aka kai wa cocin Deeper Life Bible Church da ke Otite kusa da Okene a Kogi a shekarar 2012.

Source: Twitter
Abin da ya faru a farmakin coci a Kogi
Daily Trust ta ruwaito cewa harin, wanda ya faru da safiyar 7 ga Agusta, 2012, ya yi sanadin mutuwar masu ibada sama da 19, yayin da wasu da dama suka jikkata.
A lokacin harin, wasu mutane uku dauke da bindigogin AK-47 sun buɗe wuta kan masu halartar taron nazarin Littafi Mai Tsarki a cocin.
A nan take, mutane 15 suka rasa rayukansu, yayin da ƙarin mutum huɗu suka mutu daga baya sakamakon raunukan da suka samu.
Bayan harin cocin na Okene, Abdulazeez Obadaki ya ci gaba da jagorantar wata ƙungiya da ta kai hari bankuna biyar a Uromi, Jihar Edo, inda suka kashe mutane da dama tare da sace makudan kuɗi.
Yadda DSS ta kama wanda ake tuhuma
Daga bisani jami’an tsaro sun kama shi tare da tsare shi a Gidan Gyaran Hali na Kuje, amma ya tsere a lokacin fashin magarkama da aka yi a Kuje a watan Yulin 2022.
A ranar 15 ga Nuwamba, 2025, hukumar DSS ta sanar da sake cafke Obadaki bayan dogon bincike da bibiyar diddiginsa.
Kwanaki shida bayan kama shi, DSS ta gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda aka tuhume shi da aikata laifuffuka shida da suka shafi ta’addanci.

Source: Getty Images
Lokacin da aka karanta masa tuhumar, Obadaki ya amsa laifi guda ɗaya kacal, wanda ya shafi tserewa doka, yayin da ya musanta sauran tuhume-tuhumen, cewar rahoton Vanguard.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta dage sauraron shari’ar zuwa 26 ga Janairu, 2026, tare da umarnin cewa wanda ake zargin ya ci gaba da zama a hannun DSS har zuwa ranar da za a ci gaba da shari’ar.
Hukumar DSS ta saki mutane 3
A wani labarin, kun ji cewa hukumar DSS ta bada umarnin sakin wasu mutane uku da aka tsare bisa zarginsu da ta'addanci, wanda daga baya aka gano kuskure aka yi.
Shugaban hukumar DSS na kasa, Oluwatosin Ajayi shi ya bada umarnin sakin mutanen bayan binciken hukumar ya tabbatar da ba su da laifi.
Ajayi ya amince a biya su kudin diyya na Naira miliyan uku domin tabbatar da adalci ga wadanda suka sha wahala saboda kuskuren jami’an tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

