Gwamna Ya Kawo Shirin da Zai Taimaki Matasa, Za a Raba Musu Tallafin Naira Biliyan 1

Gwamna Ya Kawo Shirin da Zai Taimaki Matasa, Za a Raba Musu Tallafin Naira Biliyan 1

  • Gwamna Babagana Zulum ya kaddamar da shirin tallafawa matasa tare da ba su horon gyaran wayar salula a jihar Borno
  • A karkashin shirin, Gwamna Zulum zai rabawa matasa tallafin kayan aikin gyaran tare da kudin da za su fara kasuwanci
  • Zulum ya ware N1bn domin rabawa wadanda suka ci gajiyar shirin, inda za a ba kowane matashi tsakanin N100,000 zuwa N1m

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ƙaddamar da wani gagarumin shirin tallafa wa matasa na Naira biliyan ɗaya (₦1,000,000,000).

Gwamna Babagana Zulum ya kirkiro shirin ne da nufin ƙarfafa tattalin arziƙin dubban matasa, musamman masu gyaran waya da sauran masu sana’o’in fasaha.

Gwamna Zulum.
Gwamna Babagana Zulum a wurin kaddamar da tallafi ga matasa a Borno Hoto: @ProfZulum
Source: Twitter

Dubban matasa za su amfana da shirin Zulum

Rahoton Leadership ya nuna cewa a karkashin shirin, za a horas da matasa 1,050 kan harkokin gyara da kula da wayoyin salula.

Kara karanta wannan

Bangarori 4 da Tinubu zai fi kashewa kudi a kasafin 2026

Sai kuma kimanin matasa 3,500 da za a koyar sana'o'i daban-daban, kuma bayan kammala horarwan, za su amfana da tallafin kuɗi kai tsaye.

Kowane matashi daga cikin wadanda aka koyar sana'ar gyaran waya, zai karɓi cikakkun kayan aiki na zamani domin su tallafa masu su dogara da kansu.

Baya ga kayan aiki, dukkan matasa 1,050 za su samu tallafin kuɗi kai tsaye a matsayin jarin fara kasuwanci.

Yadda za a raba wa matasa N1bn a Borno

An raba tallafin zuwa rukuni huɗu, rukuni na farko ya kunshi mutane 26, kowanne zai karbi tallafin Naira miliyan 1 yayin da rukuni na biyu ke da mutane 189, kowanne zai samu Naira dubu 300.

Sai kuma rukuni na uku na mutane 835, kowanne zai karɓi Naira dubu 100 sai rukuni na karshe, mai kunshe da mutum 3,500, kowanne zai karɓi Naira dubu 100 tare da kayan aiki daban-daban

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin a kasuwar wata (GSM) da ke Maiduguri, Gwamna Zulum ya ce shirin wani muhimmin mataki ne na bunƙasa rayuwar matasa.

Kara karanta wannan

An sanya ranar da Bankin Duniya zai ba Najeriya sabon rancen dala miliyan 500

“Abin farin ciki ne a gare ni tsayawa a gabanku a yau domin ƙaddamar da rabon tallafin Naira biliyan ɗaya tare da horas da matasa a kasuwar GSM ta Maiduguri. Wannan rana ce ta tarihi,” in ji gwamnan.

Gwamna Zulum ya dauki nauyin matasa 200

Ya kuma tuna da wasu manyan shirye-shiryen gwamnatinsa na zuba jari a fannin bunƙasa matasa, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Gwamna Zulum ya ce:

“Ba da daɗewa ba, wannan gwamnati ta ɗauki mataki mai ƙarfi na ɗaukar nauyin matasa 200 domin karatun tuƙin jirgin sama da injiniyan jiragen sama a Jami’ar Isaac Balami.
“Wannan shiri zai saka Borno a taswirar sufurin jiragen sama ta duniya, tare da nuna cewa duk da ƙalubalen da muke fuskanta, muna shirya matasanmu domin su yi gogayya a duniya.
Gwamna Zulum.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum a taron rabon tallafin matasa Hoto: @ProfZulum
Source: Twitter

Gwamna Zulum ya kashe N100bn a tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kashe N100bn a ayyukan tsaro da nufin kare rayukan jama'a a Borno.

Zulum wanda zai bar mulki a watan Mayun 2027 ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ban-girma ga sarkin masarautar Uba, Alhaji Ali Ibn Mamza.

Ya bayyana shirinsa na gina makarantu, cibiyar kwamfuta, cibiyar JAMB, hanyoyi da kuma kafa jami’a domin inganta rayuwar mutanen Askira/Uba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262