Bayan Takunkumin Amurka, Trump Ya Kara Saka Doka ga 'Yan Najeriya da Wasu Kasashe
- Gwamnatin Amurka ta umurci hukumar USCIS da ta dakatar da neman katin zama da na ɗan ƙasa daga Najeriya da wasu ƙasashe saboda dalilan tsaro
- Matakin ya biyo bayan wata sanarwa da shugaba Donald Trump ya rattaba wa hannu wadda ta faɗaɗa takunkumin tafiye-tafiye kan ƙasashe da dama
- Najeriya na cikin ƙasashen da aka saka ƙarƙashin takunkumin shiga kasar Amurka, lamarin da ya shafi harkokin shige da fice a tsakanin kasashen biyu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Donald Trump ya ba da umarni ga Hukumar Kula da Shige da Ficen Amurka, USCIS, da ta dakatar da karɓar bukatun neman katin zama a kasar da na zama ɗan ƙasa ga ’yan Najeriya da wasu ƙasashe.
Rahoton ya ce an ɗauki wannan mataki ne bisa dalilan tsaron ƙasa da kuma ci gaba da duba hanyoyin tantance masu neman shige da fice, musamman daga ƙasashen da aka kakabawa takunkumin tafiye-tafiye.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa matakin ya biyo bayan wata sanarwa da Shugaba Donald Trump ya sanya wa hannu, wadda ta ƙara tsaurara shigar ’yan wasu ƙasashe da Amurka ke ɗauka a matsayin masu haɗari ga tsaro da lafiyar jama’a.
Amurka ta dauki mataki kan Najeriya
A cewar bayanan da aka fitar, gwamnatin Amurka ta ce ta gano babban gibi a tsarin tantance matafiya da musayar bayanai da wasu ƙasashe ke yi.
Tribune ta rahoto sanarwar ta ce saboda waɗannan dalilai ne aka faɗaɗa takunkumin, tare da dakatar da aiwatar da wasu nau’o’in aikace-aikacen shige da fice, ciki har da neman katin zama da na ɗan ƙasa.
Kasashen da aka hana shiga Amurka
A cewar bayanan, akwai ƙasashe da aka saka ƙarƙashin cikakken takunkumin tafiye-tafiye, ciki har da Burkina Faso, Mali, Niger, South Sudan, Syria, Laos da Sierra Leone.
A bangaren takunkumin wucin gadi, jerin ƙasashen sun haɗa da Angola, Antigua da Barbuda, Benin, Côte d’Ivoire, Dominica, Gabon, Gambia, Malawi, Mauritania, Najeriya, Senegal, Tanzania, Tonga, Zambia da Zimbabwe.
Ƙasashen da Amurka ta hana katin kasa a baya
Baya ga sababbin ƙasashen da aka ƙara, akwai wasu da tun da farko suke ƙarƙashin irin takumkumin da Amurka ta kakaba musu.
Daga cikinsu akwai Afghanistan, Burundi, Chad, Cuba, Jamhuriyar Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libya, Myanmar, Somalia, Sudan, Togo, Turkmenistan, Yemen da Venezuela.
Sabuwar dakatarwar ta faɗaɗa ƙuntatawar da aka sanar a watan Yunin 2025, inda wasu ƙasashe suka fuskanci takunkumin wucin gadi.

Source: Twitter
A sabon tsarin, Laos da Sierra Leone, waɗanda a baya suke ƙarƙashin takunkumi na wucin gadi, an mayar da su zuwa cikakken takunkumi.
Amurka ta kai hari kasar Syria
A wani labarin, kun ji cewa wasu dakarun sojojin Amurka sun kai hari wani yanki na kasar Syria, sun kashe 'yan ISIS.
Donald Trump ya bayyana cewa za su cigaba da kai hare-hare Syria har sai sun ga bayan 'yan ISIS baki daya.
A makon da ya wuce ne aka rahoto cewa an kashe wasu sojojin kasar Amurka yayin wani fada da aka yi a kasar Syria.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

