Ziyarar Tinubu: Gwamnatin Bauchi Ta Aika Sako ga Mutanen Jihar

Ziyarar Tinubu: Gwamnatin Bauchi Ta Aika Sako ga Mutanen Jihar

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar ta'aziyya kan rasuwar sanannen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi
  • Gwamnatin jihar Bauchi ta fara shirye-shiryen tarbar Mai girma shugaban kasar wanda zai ziyarci jihar a ranar Asabar, 20 ga watan Disamban 2025
  • Wani hadimin Gwmana ya ce Bala Mohammed ya bukaci mutanen jihar da su zauna lafiya tare da kasancewa masu bin doka da oda yayin ziyarar

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta yi kira ga mazauna jihar da su nuna halin zaman lafiya da ladabi yayin ziyarar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kawo.

Shugaba Bola Tinubu zai kai ziyarar ne don ta'aziyya bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu.

Gwamnatin Bauchi za ta rufe tituna saboda ziyarar Tinubu
Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed da Shugaba Bola Tinubu Hoto: @SenBalaMohammed, @DOlusegun
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce wannan kiran ya fito ne a cikin wata sanarwa da Mai ba gwamna Bala Mohammed shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Juma’a, 19 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Tinubu zai je jihohi 3 kafin hutun Kirsimeti, ya fadi abin da zai kai shi

Mukhtar Gidado ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai iso jihar Bauchi ne a ranar, Asabar 20 ga watan Disamban 2025.

Me gwamnatin Bauchi ta gayawa jama'a?

A cewar sanarwar, gwamnati ta buƙaci al’umma su zauna lafiya, su bi doka da oda, tare da ba da cikakken haɗin kai ga jami’an tsaro da aka tura a faɗin jihar domin tabbatar da cewa ziyarar ta gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.

"Dangane da wannan muhimmiyar ziyara, Gwamnatin jihar Bauchi na kira ga al’umma da su kasance cikin zaman lafiya da ladabi, tare da ba da cikakken haɗin kai ga hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro da nasarar wannan ziyara ta shugaban kasa.”

- Mukhtar Gidado

Za a rufe wasu tituna a Bauchi

Gwamnatin ta kuma sanar da cewa za a rufe wasu manyan tituna da ke zuwa masallacin marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi da wasu muhimman wurare na ɗan lokaci, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar da hakan.

Gwamnatin Bauchi za ta tarbi Shugaba Bola Tinubu
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Facebook

Ta ce za a rufe su ko kuma a karkatar da zirga-zirga daga karfe 1:00 na rana zuwa karfe 6:00 na yamma, domin dalilan tsaro da tsara zirga-zirgar ababen hawa.

Kara karanta wannan

NLC: Ajaero ya fadi sabon alkawarin da Tinubu ya dauka game da rashin tsaro

An shawarci al’umma da su tsara tafiye-tafiyensu tun da wuri, su bi dokokin hanya, tare da kauce wa wuraren da aka kayyade a lokacin ziyarar shugaban kasar.

Duk da nuna nadamar duk wata damuwa da matakan ka iya haifarwa, gwamnatin jihar ta gode wa al’umma bisa fahimta da haɗin kai.

Gwamnatin Bauchi ta karawa likitoci albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Bauchi ta yi wa likitoci da sauran ma'aikatan lafiya sha tara ta arziki.

Gwamnatin ta sanar da yi musu karin albashi da kaso 100 domin inganta gudanar da ayyukansu da kuma walwalarsu.

Kwamishinan lafiya na jihar, Muhammad Sani Dambam, ya bayyana cewa amincewar ta biyo bayan la’akari da shawarwarin kwamitin musamman da aka kafa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng