Azumi Saura Wata 2, Sarkin Musulmi Ya ba da Sanarwar Duba Watan Rajab
- Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta sanar da cewa ranar Asabar, 20, Disamba, 2025, ita ce ranar duba watan Rajab na 1447AH
- An bukaci duk wanda ya ga wata da ya kai rahoto ga masarauta mafi kusa kamar wajen hakimi ko dagaci domin sanar da Sultan
- Rajab ne wata na bakwai a kalandar Musulunci daga shi kuma sai Sha’aban, sannan Ramadan da Musulmi ke azumi a cikinsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar da ke kula da harkokin addini a Masarautar Sakoto ta sanar da Musulmi a fadin Najeriya cewa za a fara duba watan Rajab na 1447AH a yau Asabar, 20, Disamba, 2025.
A cewar sanarwar, ranar da aka kayyade ta yi daidai da 29 ga watan Jumada Assaniya 1447AH. An bukaci Musulmi da su mai da hankali wajen duba watan da zarar rana ta fadi, tare da tabbatar da sahihancin abin da suka gani.

Source: Getty Images
Sanarwar da fadar Sarkin Musulmi ta fitar a Facebook ta jaddada cewa duk wanda ya ga wata, wajibi ne ya bi hanyar da aka saba domin kai rahoto ga mahukunta.
Tsarin duba wata a addinin Musulunci
Tsawon shekaru da suka gabata a tarihi, a al’adar Musulunci, duba wata muhimmin bangare ne na tabbatar da shiga sabon wata.
Hanyar da aka saba wajen duba wata a Najeriya ita ce ganin wata da ido, sannan a kai rahoto ga shugabanni da aka tanada.
Sanarwar Sultan ta bayyana cewa duk wanda ya ga sabon watan Rajab zai sanar da hakimin yankinsa ko dagacin da ke kusa da shi.
Daga nan ne rahoton zai wuce zuwa ga mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar CFR, wanda shi ne shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya.
Bayan karbar rahotanni, Sarkin Musulmi ne ke da alhakin tabbatarwa da kuma sanar da Musulmi a fadin kasar nan sakamakon duba watan.

Kara karanta wannan
Tattaunawar Buhari da Lai Mohammed a kan toshe amfani da Twitter a Najeriya a 2021
Kiran Sarkin Musulmi ga jama'a
An bukaci Musulmi da su bi wannan umarni tare da nuna hadin kai da biyayya ga tsarin da aka tanada wajen bin hanyar kai rahoto yadda ya dace na taimakawa wajen guje wa jita-jita da kuma tabbatar da sahihancin sanarwa.
A karshen sanarwar, an yi addu’a ga Allah madaukakin sarki da ya taimaka wa al’umma wajen sauke wannan nauyi yadda ya kamata, tare da neman dacewa da shiriya ga kowa da kowa.
Rajab ne wata na bakwai a kalandar Musulunci, watan da ke biye da shi kuma shi ne Sha’aban, wanda shi ne wata na takwas.

Source: UGC
Biye da shi kuma sai Ramadan, wanda shi ne wata na tara, yana da matukar muhimmanci domin a cikinsa Musulmi ke gudanar da ibadar azumi.
Sarkin Musulmi ya amince da shirya fim
A wani rahoton, kun ji cewa Mai alfarma sarkin Musulmi ya amince da shirya shim din tarihin Nana Asma'au a Najeriya.
Nana Asma'u 'ya ce ga Shehu Usman Dan Fodiyo da ya rayu a Najeriya kuma ya jagoranci kafa daular Usmaniyya.
Wacce ta nemi izinin shirya fim din, Rahama Abdulmajid ta nuna godiya game da damar da aka bata domin fito da tarihi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

