Tura Ta Kai Bango: Tinubu Ya Yi Wa Gwamnoni Barazana kan Kudin Kananan Hukumomi
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nunawa gwamnoni cewa ba da wasa yake ba kan 'yancin kananan hukumomi
- Mai girma Bola Tinubu ya bukaci gwamnonin su aiwatar da hukuncin Kotun Koli wanda ya umarci a sakarwa kananan hukumomi mara
- Shugaban kasar ya fito kai tsaye ya gayawa gwamnonin matakin da zai dauka idan har ba su aiwatar da hakan ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi gwamnonin jihohi kan kudin kananan hukumomi.
Tinubu ya gargadi gwamnonin cewa zai iya bayar da umarni domin tilasta biyan kudin kananan hukumomi kai tsaye idan suka ƙi bin hukuncin Kotun Koli.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta ce shugaban kasar ya sake yin wannan gargaɗi ne a ranar Juma’a, 19 ga watan Disamban 2025, yayin da yake jawabi a taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 15 na jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan
Bola Tinubu ya kafa sabon tsarin tsaro, ya ayyana kungiyoyi 6 a matsayin 'yan ta'adda
An gudanar da taron ne a dakin taro na fadar shugaban kasa, da ke birnin Abuja.
Wace barazana Tinubu ya yi wa gwamnoni
Tinubu ya ce rashin bin hukuncin kotu kan 'yancin kananan hukumomi na iya tilasta masa tabbatar da cewa ana biyansu kudin kai tsaye daga asusun rarraba kudi na tarayya (FAAC).
Da yake jawabi ga mambobin NEC, ciki har da gwamnonin jihohi da mambobin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC), Tinubu ya ce ya zuwa yanzu ya nuna hakuri da fahimta wajen mu’amala da gwamnonin kan batun.
"Kotun Koli ta riga ta yanke hukunci a fili, tana cewa, ‘a ba su kuɗinsu kai tsaye. Idan kuka jira sai na fitar da umarni, domin ina da wuka, ina da nama, to zan aiwatar."
“Ina nuna girmamawa da fahimta ga gwamnonina. Amma idan ba ku fara aiwatar da hukuncin ba, hujja bayan hujja, za ku gani.”
- Shugaba Bola Tinubu
Kotu ta ba kananan hukumomi 'yanci
Maganar Tinubu ta biyo bayan hukuncin Kotun Koli da aka yanke a ranar 11 ga Yulin 2024, wanda ya tabbatar da ’yancin samun kudi na kananan hukumomi.
A hukuncin da kwamitin alkalai bakwai suka yanke, kotun ta bayyana cewa saɓa wa kundin tsarin mulki ne ga gwamnatocin jihohi su rike ko su sarrafa kudin da aka tanadar wa kananan hukumomi.
Kotun ta umarci da a rika biyan kudin da ke fitowa daga asusun tarayya kai tsaye zuwa kananan hukumomi, kamar yadda sashe na 162(5) zuwa 162(8) na kundin tsarin mulki na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) ya tanada.

Source: Twitter
Tinubu ya ce dole a bi hukuncin Kotun Koli
Tinubu ya jaddada cewa bin hukuncin kotun wajibi ne ba tare da jinkiri ba, yana mai gargaɗin cewa ci gaba da yin karan tsaye ga hukuncin na iya jawo hannun gwamnatin tarayya ta dauki mataki, jaridar The Punch ta kawo labarin.
"Babban abin da ya kamata mu yi biyayya da shi shi ne hukuncin Kotun Koli. Dole ne mu bi shi. Dole ne mu girmama hukuncin.”
- Shugaba Bola Tinubu
Tinubu ya tuna baya kan zaben 2023
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tuna baya kan kalubalen da ya fuskanta gabanin zaben 2023.

Kara karanta wannan
Kungiyar CAN ta yi magana da babbar murya ga Tinubu yayin da ake shirin Kirsimeti
Mai girma Bola Tinubu ya ce ya sha bakar wahala da tsallake tarkuna kafin samun nasara a zaben 2023 da ta gabata.
Shugaban kasar ya bayyana gwamnoni guda biyu na sane da irn wahalar da ya sha tun daga batun sauya fasalin Naira da layuka masu tsawo da aka rika samu a gidajen mai.
Asali: Legit.ng
