Majalisa Ta Ki Amincewa da Kudirin Hukunta Masu Sayan Kuri’u a Zabe
- Majalisar Wakilai ta ƙi amincewa da kudirin da ake ganin zai kawo sauyi kan magudin zabe a fadin Najeriya baki daya
- Kudirin da aka ki amincewa zai mayar da ba wa wakilai kuɗi ko kayayyaki a zaɓen fidda gwani na jam’iyyu a matsayin laifi
- ’Yan majalisar sun yi watsi da kudirin ne yayin tattaunawar gyaran Dokar Zaɓe ta 2022, inda aka nemi daurin shekaru biyu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Majalisar Wakilai ta yi watsi da wani kudiri da aka kawo yayin zamanta domin tsaftace harkokin zabe a Najeriya.
Majalisar ta ƙi amincewa da kudirin da ke neman mayar da ba wa wakilan jam’iyya kuɗi ko wasu kayayyaki domin rinjayar zaɓen fitar da gwani a matsayin laifi.

Source: Facebook
Kudirin da majalisa ta yi watsi da shi
’Yan majalisar sun kaɗa ƙuri’a ne yayin nazari sashe-sashe na rahoton da ke neman gyara Dokar Zaɓe ta 2022, inda suka yi watsi da kudirin baki ɗaya, cewar TheCable.
Wani sashe na rahoton ya tanadi cewa duk wanda ya ba wakili kuɗi ko wata alfarma domin canza sakamakon zaɓen fitar da gwani, zai fuskanci ɗaurin shekaru biyu ba tare da zaɓin tara ba.
Sashe na 89(4) na rahoton gyaran dokar ya ce:
“Duk wanda ya ba wakili kuɗi ko kayayyaki domin rinjayar sakamakon fidda gwani, taro ko babban taron jam’iyya, ya aikata laifi kuma zai fuskanci ɗaurin shekaru biyu ba tare da tara ba.”
Sai dai dukkan ’yan majalisar sun ƙi wannan sashe bayan da Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu, ya nemi a yi ƙuri’a, cewar The Guardian.
Ba wa wakilan jam’iyya kuɗi ko kayayyaki domin rinjayar zaɓe abu ne da ya zama ruwan dare a zaɓukan fitar da gwani a Najeriya, inda ’yan takara ke amfani da kuɗi domin samun nasara.

Source: Facebook
Wuraren da majalisar ta amince da su a kudirin
A wani bangare kuma, Majalisar Wakilai ta amince da wani sashe daban da ya tanadi tsauraran hukunci kan laifuffukan takardun ƙuri’a da kayan zaɓe.
A ƙarƙashin sabon sashe, duk wanda ba tare da izini ba ya buga takardar ƙuri’a, ko takardar sakamakon zaɓe, ko ya buga fiye da adadin da hukumar INEC ta amince da shi, ko aka same shi da irin waɗannan takardu yayin da zaɓe ke gudana, ya aikata laifi.
Haka kuma, duk wanda ya ƙera, ya shigo da, ya mallaka ko ya yi amfani da akwatin zaɓe ko wata na’ura da za ta ba da damar ɓoye, karkatarwa ko magudin ƙuri’a, zai fuskanci tarar kuɗi har Naira miliyan 75, ko ɗaurin shekaru 10 a gidan yari, ko duka biyun.
Tinubu ya mika kasafim kudi ga majalisa
Kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2026 a zaman hadin gwiwa na majalisun tarayya.
Tinubu ya yi bayani dalla-dalla kan yadda Najeriya za ta kashe sama da Naira tiriliyan 58 a shekara mai zuwa watau 2026.
Daga ciki, bangaren tsaro ne ya fi samun kaso mafi tsoka a kasafin kudin, wanda aka ware sama da Naira tiriliyan 15 don biyan basussuka.
Asali: Legit.ng

