Bola Tinubu Ya Kafa Sabon Tsarin Tsaro, Ya Ayyana Kungiyoyi 6 a matsayin 'Yan Ta'adda

Bola Tinubu Ya Kafa Sabon Tsarin Tsaro, Ya Ayyana Kungiyoyi 6 a matsayin 'Yan Ta'adda

  • Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta fara aikin kafa sabon tsarin tsaron kasa domin murkushe ta'addanci gaba daya
  • Shugaban kasar ya jero wasu kungiyoyi da suka dauki makamai, ya ce daga yanzu dukansu za a dauke su a matsayin 'yan ta'adda
  • Tinubu ya bai wa 'yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa daga yanzu duk wata ƙungiya ko mutune da ke ɗauke da makamai ba tare da lasisi ba, za a riƙa ɗaukar su a matsayin ’yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Tsaro ne kan gaba da Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2026 a Majalisa

Shugaba Tinubu ya lissafo wasu shida daga cikin irin wadannan kungiyoyi, yana mai cewa dukansu za a dauke su a matsayin 'yan ta'adda a karkashin sabon tsarin tsaro na gwamnatinsa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a taro Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta ce shugaban ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’a yayin gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 ga zaman haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Kungiyoyin da Tinubu ya ambata a Majalisa

Tinubu ya ce a sabon tsarin tsaro ’yan bindiga, ƙungiyoyin asiri, mayakan sa-kai, ƙungiyoyin ‘yan daba masu dauke da makamai, 'yan fashin daji, da sojojin haya daga waje ba za a ƙara kallon su a matsayin masu laifi na gama-gari ba.

Shugaban kasar ya ce duka wadannan kungiyoyi da ya ambata za a ɗauke su a matsayin barazana ta ta’addanci ga zaman lafiyar Najeriya.

“Za mu buɗe sabon babi a tsarin shari’ar aikata laifuffuka. Ba za mu nuna tausayi ga duk wanda ya aikata ko ya tallafa wa ta’addanci, fashi da makami, sace mutane ko wani laifi na tashin hankali ba,” in ji Tinubu.

Gwamnatin Tinubu ta canza tsarin tsaro

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya gargaɗi gwamnoni game da tsaro a bukukuwan kashen shekara

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa na sake fasalin tsarin tsaron ƙasa gaba ɗaya tare da kafa tsarin yaƙi da ta’addanci, wanda ya dogara da hada bayanan sirri, haɗin gwiwar al’umma, da dabarun yaƙi da tayar da ƙayar baya.

“Wannan sabon tsari zai sauya gaba ɗaya yadda muke fuskantar ta’addanci da sauran laifuffukan tada zaune tsaye,” in ji shugaban.

Tinubu ya bayyana cewa sabon tsarin zai haɗa dukkan ayyukan yaƙi da ta’addanci ƙarƙashin tsari guda na jagoranci, domin tabbatar da saurin ɗaukar mataki.

Shugaban kasa, Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a Majalisar Tarayya Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta tsaya kan masu aikata laifuffuka kaɗai ba, za ta fuskanci masu ɗaukar nauyinsu da masu ba su tallafi.

Shugaban ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar maido da doka da oda a duk faɗin ƙasar nan, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2026

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2026 ga Majalisar Tarayya a Abuja.

Bola Tinubu ya bayyana cewa kasafin kudin zai lakume sama da Naira tiriliyan 58, inda ya ce an ware wa bangaren tsaro kaso mafi tsoka.

Ya ce an ware Naira tiriliyan 26.08 domin gudanar da ayyukan ci gaba, yayin da aka ware Naira tiriliyan 15.25 a matsayin kudin tafiyar da gwamnati na yau da kullum.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262