Hukumar INEC Ta Shiga tsakani a Rikicin da Ya Dabaibaye PDP, Ta Kira Bangarori 2
- Hukumar INEC ta fara kokarin samar da masalaha da sulhu tsakanin bangarorin jam'iyyar PDP da ke adawa da juna
- Shugaban INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan ya gayyaci kowane bangare zuwa wurin wani taron sulhu a hedkwatar hukumar da ke Abuja
- Amupitan ya ce INEC ta kira wannan zama ne bayan samun wasiku masu cin karo da juna daga jam'iyyar adawa ta PDP
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tsoma baki kan rigingimun cikin gida na jam'iyyar PDP, wanda ya kai ga darewarta zuwa gida biyu.
Jam'iyyar PDP dai ta jima tana fama da rigingimu kala daban-daban, amma a baya-bayan nan, kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) ya dare gida biyu.

Source: Twitter
INEC ta shiga ganawa da bangarorin PDP
Sai dai a yau Juma'a, 19 ga watan Disamba, 2025, hukumar INEC ta gayyaci bangarorin PDP biyu da ke adawa da juna domin kawo sulhu da masalaha a jam'iyyar, in ji rahoton Vanguard.
INEC ta gayyaci bangarorin jam’iyyar PDP biyu da ke takaddama zuwa wurin wani taron sulhu na musamman da ta shirya domin warware duk wata matsala a hedikwatarta da ke Abuja.
Taron, wanda ke gudana a halin yanzu, ya haɗa bangaren da Tanimu Turaki (SAN) ke jagoranta da kuma bangaren Abdulrahman Mohammed da ke samun goyon bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.
Rahotanni sun nuna cewa Tanimu Turaki ya halarci taron tare da wasu mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC), ma’aikatan sakatariyar PDP da kuma tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu.
Daily Trust ta tattaro cewa a daya ɓangaren, Abdulrahman Mohammed ya isa taron tare da mambobin kwamitin rikon kwarya na ƙasa, ciki har da Sakataren kwamitin, Sanata Sam Anyanwu.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta binciko gaskiya, ta kori manyan jami'ai 38 daga aiki a NSCDC
Me yasa INEC ta shirya sulhunta PDP?
Ana sa ran taron zai taimaka wajen warware rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar PDP, tare da samar da hanyar da za ta tabbatar da daidaito da zaman lafiya a cikin jam’iyyar.
Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) ya ce an kira wannan zama ne bayan "wasiku masu karo da juna" da hukumar ta samu daga PDP.

Source: Twitter
Ya jaddada kudurin hukumar na tabbatar da tsabta da tsari yayin da shirye-shiryen zaɓen da za a yi a babban birnin tarayya da kuma na 2026 ke kara gabatowa.
Shugaban INEC ya ce hukumar ta yanke shawarar gayyatar shugabannin PDP su "haɗa kai" su tsara hanyar da za a bi, yana mai nuna gamsuwarsa da cewa jagorori daga ɓangarorin biyu sun halarci taron domin tattaunawa.
PDP ta soki sauya shekar Gwamna Fubara
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta ce sauya sheƙar Gwamna Simi Fubara zuwa APC tamkar ji wa kansa rauni ne tare da jefa kansa a cikin matsala.
PDP ta ce duk wanda ya bi labarin rikicin siyasar Rivers zai gane cewa gwamna Fubara ne ya jagoranci kansa zuwa halin da ya ke ciki a yanzu.
PDP ta kara jaddada cewa sauya sheƙar Fubara ya sake tabbatar daNkoma bayan dimokuraɗiyya a Najeriya, musamman yadda jam’iyya maiNmulki ke ƙoƙarin mai da kasar jam’iyya ɗaya.
Asali: Legit.ng

