Majalisa Ta Yi Na'am a Kashe Masu Garkuwa da Mutane, Gwamnati Ta Ki Yarda

Majalisa Ta Yi Na'am a Kashe Masu Garkuwa da Mutane, Gwamnati Ta Ki Yarda

  • Babban Lauyan Ƙasa, Lateef Fagbemi ya yi fatali da shirin majalisa na hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane ba tare da zabin tara ba
  • Fagbemi ya gargadi cewa hakan na iya hana kasashen waje mika wadanda ake zargi da ta’addanci zuwa Najeriya
  • Ya ce hukuncin kisa na iya ƙara tsananta tsattsauran ra’ayi, ya jefa tsarin shari’a cikin barazana, tare da cunkoson gidajen yari

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya nuna adawa da shirin Majalisar Dattawa na gyara dokar yaki da ta’addanci.

Majalisa ta amince da akaba hukuncin kisa ba tare da zabin tara ba ga duk laifuffukan da suka shafi ta'addancin garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya gargaɗi gwamnoni game da tsaro a bukukuwan kashen shekara

Gwamnati ta ki amincewa da kashe 'yan ta'adda
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa Fagbemi ya bayyana cewa irin wannan gyara na iya lalata hadin gwiwar Najeriya da kasashen duniya a yaki da ta’addanci.

Gwamnati ta magantu kan kashe 'yan ta'adda

Ministan ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis yayin taron sauraron ra’ayoyin jama’a kan kudirin gyaran Dokar Hana Ta’addanci da kuma soke da sake gabatar da Dokar Masu Aikin Lauya.

Taron ya gudana ne karkashin kwamitocin Majalisar Dattawa kan Hakkokin Dan Adam da Harkokin Shari’a, Tsaro da Leken Asiri, da kuma Harkokin Cikin Gida.

A cewar Fagbemi, kasashe da dama ba sa amincewa da mika wadanda ake zargi da aikata manyan laifuffuka idan suna fuskantar hukuncin kisa.

Ya ce hakan na iya sa Najeriya ta zama kasa mai wahalar samun hadin kai a bangaren musayar bayanai da mika masu laifi.

Ya ce:

“Idan muka saka hukuncin kisa, muna iya haifar da mafaka a kasashen waje ga manyan masu shirya ta’addanci, domin kotunan waje kan toshe mika su bisa hujjar kare hakkin dan Adam."

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Shugaban Majalisa, Akpabio ya ambato masu hana Najeriya zaman lafiya

Dalilan gwamnati da gargadin tsaro

Fagbemi ya bayyana cewa matsayar gwamnati ta ta’allaka ne kan cikakken nazari na shari’a, dabarun tsaro da kuma hakkin dan Adam.

Ya bukaci ‘yan majalisa da su sake duba kudirin, yana mai cewa hukuncin kisa na iya ƙarfafa tunanin 'shahada' a tsakanin ‘yan ta’adda, wanda hakan ke taimaka musu wajen daukar karin mabiya.

Lateef Fagbemi ya ce ya kamata a guji ba wa ‘yan ta’adda abin da za su yi amfani da shi wajen tayar da hankulan jama’a da kara daukar mambobi.

Haka kuma, Fagbemi ya nuna damuwa kan yadda gwamnonin jihohi ke kin sanya hannu kan takardun kisa saboda dalilai na addini, siyasa ko dabi’a.

Ya ce hakan ya haifar da wani yanayi na dakatar da hukuncin kisa a aikace, inda masu laifi ke shafe shekaru a kurkuku ba tare da kammala hukuncinsu ba.

Kotu ta soke afuwar gwamnatin Tinubu

A wani labarin, mun wallafa cewa kotun koli ta Najeriya ta rusa afuwar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, wacce aka samu da laifin kashe mijinta, marigayi Bilyaminu Atiku.

Kara karanta wannan

Malami: EFCC ta kai samame gidan da 'yar marigayi Buhari ke zaune

A hukuncin da kotun ta yanke, ta tabbatar da hukuncin kisa da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a kanta tun a shekarar 2020, bayan an tabbatar da cewa ta kashe Maigidanta.

Rahotanni sun tabbatar da cewa alkalai hudu ne suka yanke wannan hukunci, inda suka yi ittifaki kan cewa hukuncin kisan da aka yanke wa Maryam Sanda a baya ya dace da doka, kuma babu hujjar soke shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng