An Fadi Wadanda ba za Su Fara Biyan Haraji ba karkashin Dokar Tinubu a 2026

An Fadi Wadanda ba za Su Fara Biyan Haraji ba karkashin Dokar Tinubu a 2026

  • Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa kamfanoni 149 da ke cin gajiyar hutun haraji za su ci gaba da amfana da shi na akalla karin shekaru biyu
  • Matakin na zuwa ne yayin da Najeriya ke shirin aiwatar da sabon tsarin haraji daga Janairu, 2026, ba tare da karya yarjejeniyar da aka riga aka kulla ba
  • Rahotanni sun nuna cewa hukumar NIPC ta ce tsarin zai kare masu zuba jari tare da sauya tsarin hutun zuwa sabon salo na karfafa tattalin arziki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa kamfanoni 149 da ke cin gajiyar tsarin rashin biyan haraji za su ci gaba da samun hutun haraji, duk da shirin fara sabon tsarin haraji a kasar daga Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Trump: Sashen kamfanin Tiktok zai koma karkashin kulawar Amurka

Wannan bayanin ya fito ne daga hukumar kula da zuba jari ta Najeriya, NIPC, wadda ta ce an tanadi matakan sauyi domin kare kamfanonin da aka riga aka amince da su a karkashin tsohon tsari.

Shugaban gyaran haraji, Taiwo Oyedele
Shugaban kwamitin gyaran harajin Bola Tinubu. Hoto: Taiwo Oyedele
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa gwamnatin ta bayyana cewa manufar ita ce tabbatar da kwarin gwiwar masu zuba jari, tare da kauce wa girgiza harkokin kasuwanci yayin da ake sauya tsarin haraji.

Dalilin ci gaba da hutun haraji a 2026

Shugaban Kwamitin gyaran haraji na fadar shugaban kasa, Taiwo Oyedele, ya ce an yanke shawarar barin kamfanonin da ke da takardar shaida su kammala wa’adin hutunsu.

Ya ce wannan mataki yana da muhimmanci domin nuna cewa gwamnati na mutunta alkawurra da yarjejeniyoyin da ta riga ta kulla da masu zuba jari.

Tinubu da shugaban gyaran haraji
Shugaban gyaran haraji da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Taiwo Oyedele|Bayo Onanuga
Source: UGC

A cewarsa, kamfanonin za su ci gaba da samun rangwamen haraji na akalla shekaru biyu, maimakon a katse musu shi kai tsaye da zarar sabuwar doka ta fara aiki.

Bayanan NIPC kan hutun haraji

Wata jami’ar sashen kula da manufofin tallafi a NIPC, Uchenna Okonkwo, ta bayyana cewa daga shekarar 2017 zuwa zango na biyu na shekarar 2025, an samu bukatu 693 na neman shiga hutun haraji.

Kara karanta wannan

Bayan suka ta ko ina, an dakatar da yi wa dogarin Shugaba Tinubu karin girma

Daga cikin wadannan, an amince da 304, an ki yarda da 64, sannan an soke takarda guda daya kacal, lamarin da ya bar kamfanoni da dama a matsayin masu cin gajiyar shirin.

Vanguard ta rahoto cewa shirin na bai wa kamfani cikakken rangwamen haraji na tsawon shekaru uku, tare da yiwuwar kara masa wasu shekaru biyu idan an cika sharuda.

Sabon tsarin hutun haraji da aka fitar

A karkashin sabon dokar haraji, shirin zai koma tsarin da ake kira Economic Development Incentive, wanda zai mayar da hankali kan biyan haraji tare da samun rangwamen kudi ta hanyar jarin da kamfani ke sake zubawa.

A sabon tsarin, kamfanoni za su biya haraji amma za su samu rangwame bisa yawan jarin da suka zuba, wanda zai iya kai wa har shekaru 15 idan an ci gaba da hada-hada.

IPMAN ta ce kudin man fetur zai ragu

A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar dillalan man fetur ta kasa, IPMAN, ta shiga yarjejeniya da matatar Dangote.

IPMAN ta bayyana cewa yarjejeniyar da ta kulla da Dangote za ta jawo karyewar farashin mai a fadin Najeriya.

Shugaban kungiyar ya yi kira ga dukkan wadanda ke karkashin IPMAN da su fifita sayen man fetur daga matatar Dangote.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng