Babban Fasto, Hassan Kukah Ya Sa Labule da Jagoran IPOB Kanu a Kurkukun Sokoto
- Bishof Matthew Kukah ya kai ziyara gidan gyaran hali na Sakkwato gabanin bikin Kirsimeti da ke tafe a ranar 25 ga watan Disamba, 2025
- Faston ya gana da Nnamdi Kanu da sauran fursunoni, kuma ya kare tattaunawar da suka yi ba tare da la'akari da laifin da ya aikata ba
- Wasu daga cikin fursunonin da ke gidan maza da ya gana da su sun bayyana damuwarsu, tare da neman ya mika kokensu domin a agaza masu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sakkwato – Babban limamin Cocin Katolika a Sakkwato, Most Rev. Matthew Hassan Kukah, ya kai ziyara Gidan Gyaran Hali na jihar inda ta gana da Nnamdi Kanu.
Ziyarar da ya kai a ranar Alhamis na zuwa a matsayin wani bangare na shirin ziyarar Kirsimeti da ya saba yi duk shekara.

Source: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa a yayin ziyarar, Bishop Kukah ya gana da fursunoni da dama, ciki har da shugaban ƙungiyar IPOB da aka haramta, Nnamdi Kanu.
Bishof Mathew Kukah ya gana da Nnamdi Kanu
Daily Post ta ruwaito cewa da yake tabbatar da ziyarar a wata tattaunawa ta wayar tarho, Bishof Kukah ya bayyana dalilin ganawarsa da dukkannin fursunonin, ba tare da la’akari da laifinsu ko matsayinsu ba.
Ya yi bayanin cewa ganawar ta samo asali ne daga wajibcin aikinsa na addini. Ya bayyana cewa Cocin Katolika ba ta mai da hankali kan laifin mutum ba, sai dai kan mutuncinsa a matsayin ɗan Adam.
A cewar babban faston:
“Babu wani abu da ya saɓa wa doka ko addini a ziyarar da na kai masa, domin ina da nauyin kula da kowa da ke ƙarƙashin hidimata ta addini. Mu muna duba mutane ne, ba yanayinsu ko laifinsu ba. Ba mu zama alkalan mutane ba.”
Ya ƙara da cewa ziyarar gidajen gyaran hali a lokacin Kirsimeti ta zama al’ada a gare shi, inda yake shiga domin tattaunawa da fursunoni, sauraron damuwarsu.
Mathew Kukah ya aika sako ga fursunoni
A wata sanarwa da Diocese of Sokoto ta fitar, an bayyana cewa Bishof Kukah ya kai ziyarar ne tare da wasu firistoci, ‘yan uwa mata na addini da kuma wasu 'yan Cocin Katolika.
Tawagar ta samu tarba daga Shugaban Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya reshen Jihar Sakkwato, tare da manyan jami’ansa.

Source: UGC
Sanarwar, wadda Daraktan Sadarwa na Diocese, Pascal Salifu, ya sanya wa hannu, ta ce Bishof Kukah ya gudanar da zaman sauraro na musamman da fursunonin maza da mata.
A wadannan zaman, fursunoni sun bayyana halin da suke ciki, ƙalubalen rayuwa a gidan yari da kuma damuwarsu kan yanayin tsarewa.
Wasu daga cikin fursunonin sun koka kan tsare su na dogon lokaci ba tare da shari’a ba, inda suka bayyana kansu a matsayin marasa laifi tare da roƙon a taimaka a kai ƙorafensu ga hukumomin da suka dace.
Kotu ta yanke hukunci kan bukatar Kanu
A wani labarin, mun wallafa cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da wata buƙata da jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya shigar a gabanta game da tsare shi.
Kanu ya bukaci a dauke shi daga gidan gyaran hali na Sakkwato zuwa wani gidan gyaran hali da ke babban birnin tarayya Abuja ko jihar Nasarawa, domin ya samu damar bin diddigin shari’arsa yadda ya kamata.
Alkalin kotun, James Omotosho, ya yi watsi da bukatar a ranar Litinin, 8 ga watan Disamba, 2025, inda ta ce ba za a iya bayar da irin wannan umarni ba sai an saurari bangaren gwamnatin tarayya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


