Tinubu bai Ce Uffan ba, Majalisa Za Ta Binciki Zargin Canza Dokar Haraji Ta Bayan Fage

Tinubu bai Ce Uffan ba, Majalisa Za Ta Binciki Zargin Canza Dokar Haraji Ta Bayan Fage

  • Majalisar Wakilai ta kafa kwamitin bincike kan sabanin da aka samu a dokokin harajin da gwamnatin Najeriya ta sanya wa hannu
  • Wasu 'yan majalisa sun gano cewa abin da aka sanya hannu da kuma wallafa wa ya bambanta da abin da ‘yan majalisa suka amince da shi
  • Duk da cece-kucen da batun ya jawo, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ki cewa komai a kan sabanin da aka samu a dokar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Fadar Shugaban Kasa ta yi shiru a kan zargin da ke cewa akwai sabani tsakanin dokokin haraji da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da su da kuma sigar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu .

Kara karanta wannan

Babban Fasto, Hassan Kukah ya sa labule da jagoran IPOB Kanu a kurkukun Sokoto

Gwamnatin tarayya ta wallafa sababbin dokokin haraji domin jama'a su gani, amma 'yan majalisa sun gano akwai sabani tsakanin wanda aka wallafa da wanda majalisa ta amince da shi.

Majalisar wakilai ta fara binciken sabani a dokar haraji
Wasu daga cikin 'yan majalisar wakilai Hoto; House of Representatives
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa wannan batu ya taso ne bayan wani dan Majalisar Wakilai, AbdulSamad Dasuki na PDP daga Sakkwato ya dauko zancen a zauren majalisar a ranar Laraba.

Majalisa ta gano matsala a dokar haraji

TVC News ta wallafa cewa AbdulSamad Dasuki ya bayyana cewa dokokin harajin da aka wallafa a mujallar gwamnati ba su yi daidai da abin da ‘yan majalisa suka tattauna da aminta da su ba.

'Dan majalisar ya bukaci majalisar ta dauki wannan batu da muhimmanci, ganin cewa yana da nasaba da mutuncin majalisa da tsarin dimokuraɗiyya.

Gwamnatin Tinubu ta ki cewa komai bayan gano kuskure a dokar haraji
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sai dai gwamnatin tarayya ta yi gum a bakinta domin masu bai wa Shugaban Kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga da Daniel Bwala, ba su ce komai ba.

Majalisa ta kafa kwamiti kan dokar haraji

Biyo bayan wannan zargi, Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya kafa wani kwamitin wucin gadi na mutum bakwai domin bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

Majalisa ta ɗauki mataki kan wani mamba da aka gano ya naɗi sautin zaman sirri

Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Hon. Muktar Aliyu Betara, yayin da Ahmed Idris Wase, Sada Soli, James Abiodun Faleke, Fred Agbedi, Babajimi Benson da Iduma Igariwey.

A hannu guda kuma jam'iyyar adawa ta PDP ta bukaci a gudanar da bincike mai zurfi kan zargin sabanin da ke cikin dokar haraji.

A wata sanarwa da Sakatarenta na Yada Labarai na Ƙasa, Ini Ememobong, ya fitar, jam’iyyar ta bayyana cewa sabanin da aka samu babbar barazana ce.

PDP ta bukaci a dage fara aiwatar da dokar haraji daga ranar 1 ga Janairu, 2026, na tsawon akalla watanni shida domin a kammala bincike da wayar da kan jama’a.

An gano matsala a dokar haraji

A baya, mun wallafa cewa wani dan Majalisar Wakilai, Abdussamad Dasuki, ya ja hankalin ‘yan majalisa kan zargin cewa an yi sauye-sauye a dokokin haraji bayan Majalisar Tarayya ta amince da su.

Kara karanta wannan

Kotu ta gindaya sharudda masu tsauri kafin sakin Ministan Buhari, Ngige

Dasuki ya ce dokokin da aka wallafa a hukumance sun bambanta da waɗanda Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa suka tattauna tare da amincewa da su, bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da su.

'Dan majalisar ya bayyana hakan ne a zaman majalisa na ranar Laraba, 17 ga watan Disamba, 2025, yana mai cewa an take masa hakki a matsayinsa na wakilin jama’a, bayan sun yi aikinsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng