'Matatar Dangote za Ta Jawo Ragin Farashin Man Fetur a Najeriya,' IPMAN

'Matatar Dangote za Ta Jawo Ragin Farashin Man Fetur a Najeriya,' IPMAN

  • Rahotanni sun nuna cewa kungiyar IPMAN ta umarci mambobinta a fadin Najeriya da su fifita sayen mai daga matatar Dangote da ke jihar Legas
  • Kungiyar ta bayyana farin cikinta kan yarjejeniya da matatar Dangote ta fara kan kai man fetur kai tsaye kuma kyauta ga abokan huldarta a Najeriya
  • IPMAN ta ce wannan hadin gwiwa zai kara rage farashin man fetur, tare da tabbatar da wadatar mai ba tare da tangarda ba a sassan kasar nan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Kungiyar IPMAN ta ce fara samar da man fetur daga matatar Dangote ga mambobinta kai tsaye zai taimaka matuka wajen rage farashin fetur a Najeriya.

Kungiyar ta bayyana cewa ta riga ta yi yarjejeniya da matatar Dangote domin fara sayar da mai ga ’yan IPMAN kai tsaye, tare da jigilar kaya kyauta zuwa gidajen mai a duk fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

EFCC ta cafke bokaye da kudin kasashen waje na boge bayan damfarar 'yan Najeriya

Alhaji Aliko Dangoote
Dangote da wasu motocin dakon mai. Hoto: Dangote Industries
Source: Twitter

Vanguard ta ce bayanin na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban IPMAN na kasa, Alhaji Abubakar Maigandi Shettima, ya fitar, inda ya ce matakin zai kara karfafa wadatar fetur tare da rage farashi ga al’umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

IPMAN za ta fifita matatar Dangote

A cikin sanarwar, Shettima ya ce IPMAN na da tasiri sashen rarraba mai a Najeriya, inda ya bayyana cewa sama da kashi 80 cikin 100 na kasuwar sayar da fetur na hannun mambobin kungiyar.

Ya ce bisa wannan matsayi, IPMAN ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ba za a samu karancin fetur ba, la’akari da tsarin hadin gwiwa da matatar Dangote.

Shettima ya ce fara jigilar mai kyauta zuwa tashoshin man fetur na mambobin IPMAN daga Janairun, 2026, zai sake rage kudin da ’yan kasuwa ke kashewa, lamarin da zai kai ga saukar farashin fetur.

Dalilan IPMAN kan rage farashin fetur

Shugaban IPMAN ya bayyana cewa matatar Dangote ta bayar da mafi saukin farashi ga ’yan kasuwa idan aka kwatanta da sauran hanyoyin samar da fetur.

Kara karanta wannan

Jirgin ruwan Najeriya da wasu kasashe da suka fada tarkon Amurka a 2025

Ya ce wannan ne ya sa kungiyar ke kira ga dukkan mambobinta a fadin kasar nan da su fifita sayen mai daga matatar Dangote, domin hakan zai taimaka wajen saukaka wa ’yan Najeriya radadin tsadar man fetur.

Shettima ya kara da cewa IPMAN ta dade tana kira da a zurfafa tace man fetur a cikin gida, yana mai cewa dogaro da shigo da fetur daga kasashen waje ba tsari ba ne mai dorewa ga tattalin arzikin kasa.

Matatar Aliko Dangote
Wani sashe na matatar Dangote da ke Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: UGC

Hadakar IPMAN da matatar Dangote

Sanarwar ta ce hadin gwiwar IPMAN da matatar Dangote na da manufa daya tilo, wato inganta rayuwar ’yan Najeriya ta hanyar wadatar man fetur da rage farashi.

Kungiyar ta yaba da rawar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taka wajen goyon bayan manufofin tace man fetur a cikin gida, tare da sake fasalin shugabanci a hukumomin NMDPRA da NUPRC.

Shugaban NMDPRA ya yi murabus

A wani labarin, kun ji cewa shugaban hukumar man fetur da NMDPRA, Farouk Ahmed ya ajiye aiki bayan sabani da Aliko Dangote.

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus dinsa tare da maye gurbinsa nan take.

Kara karanta wannan

Rikici ya kaure a tsakanin yan kasuwa, ana gasar rangwamen farashin fetur

Dangote da shugaban NMDPRA sun fara sabani ne game da bayar da lasisin shigo da man fetur daga kasashen waje zuwa Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng