Daga Shugaban Kasa zuwa Kansila: Kudin Kamfen da Za a Iya Kashewa a Najeriya
- Majalisar wakilai ta amince da ƙara kuɗin kamfen da za a iya kashewa ga ’yan takarar shugaban ƙasa da na gwamna a ƙarƙashin dokar zaɓe
- Hakan na zuwa ne yayin da majalisar ta amince da wasu gyare-gyare da suka shafi dokokin zaben Najeriya, musamman ganin 2027 na karatowa
- Masana siyasa sun nuna damuwa cewa tsadar kudin kamfen na iya ƙara nesanta talakawa daga tsarin dimokuraɗiyya ko da suna da nagarta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Majalisar wakilai ta ɗauki mataki mai muhimmanci wajen sauya tsarin kuɗin kamfen a Najeriya, inda ta ƙara adadin kuɗin da ’yan takara ke da damar kashewa.
Wannan mataki ya biyo bayan amincewa da dokar zaɓe ta 2025, bayan nazari sashe bayan sashe kan rahoton kwamitin majalisa na harkokin zaɓe, ƙarƙashin jagorancin Adebayo Balogun.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an dauki wasu daga cikin matakan ne domin kara kawo gyara a harkokin zaben Najeriya.
An kara kuɗin kamfen a manyan kujeru
A ƙarƙashin sashe na 93(2) da aka amince da shi, majalisar ta ƙara adadin kuɗin kamfen na ’yan takarar shugabancin ƙasa daga Naira biliyan 5 zuwa Naira biliyan 10.
Haka kuma, rahoton ya nuna cewa kuɗin kamfen na ’yan takarar gwamna ya tashi daga Naira biliyan 1 zuwa Naira biliyan 3.
Ba a nan kawai aka tsaya ba, domin majalisar ta kuma kara adadin kuɗin kamfen ga ’yan takarar majalisar kasa.
’Yan takarar Sanata yanzu za su iya kashe har Naira miliyan 500, maimakon Naira miliyan 100 da aka tanada a baya.
A bayanin da ta fitar, ’yan takarar majalisar wakilai kuma an kara musu adadin kudin daga Naira miliyan 70 zuwa Naira miliyan 250.
Rahoton Trust Radio ya ce ga ’yan takarar majalisun jihohi, an ƙara musu adadin kuɗin kamfen daga Naira miliyan 30 zuwa naira miliyan 100.
A matakin ƙananan hukumomi, An kara kudin daga Naira miliyan 30 zuwa Naira miliyan 60, yayin da ’yan takarar kansila aka ƙara musu daga Naira miliyan 5 zuwa Naira miliyan 10.
An takaita gudumawar kuɗin kamfen
Majalisar ta kuma amince da tanadin da ke takaita gudummawar kuɗi daga mutum ɗaya ko kamfani zuwa Naira miliyan 500 ga kowane ɗan takara.
Bugu da ƙari, gyaran dokar ya tanadi wajabcin INEC ta rika aikawa da sakamakon zaɓe ta yanar gizo kai tsaye, domin ƙara gaskiya da amincewa da sakamakon zaɓe.

Source: Facebook
Ra’ayoyin masana kan kudin kamfen
Sai dai masana siyasa sun fara bayyana damuwa kan wannan sauyi. masani a fannin kimiyyar siyasa, Farfesa Gbade Ojo, ya ce karin kudin na iya fasalin dimokuraɗiyyar Najeriya gaba ɗaya.
A cewarsa, irin wannan mataki na nuni da cewa dimokuraɗiyya na ƙara fita daga hannun talakawa zuwa hannun masu kuɗi.
Ya ce hakan na hana ƙwararrun ma’aikatan gwamnati masu gogewa shiga siyasa, duk da irin gudummawar da za su iya bayarwa ga ƙasa.
An gyara wasu dokokin zaben Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa Majalisar wakilai ta amince da wasu gyare-gyare a dokar zabe ta kasa.
Daga cikin gyaran da aka yi akwai sake fasalin gudanar da shari'a kan matsalar da jam'iyyu suka samu kafin zabe.
Baya ga haka, majalisar ta tanadi hukuncin dauri ga jami'an INEC da aka samu da taimakawa wajen magudi a zabuka.
Asali: Legit.ng


