Masu Garkuwa da Mutane Sun Bude wa 'Yan Sandan Najeriya Wuta, An Rasa Rayuka

Masu Garkuwa da Mutane Sun Bude wa 'Yan Sandan Najeriya Wuta, An Rasa Rayuka

  • ’Yan sanda sun kashe masu garkuwa bayan wani kazamin artabu a jihar Rivers, yayin da miyagun ke kokarin raba kudin fansa
  • An rahoto cewa 'yan sanda sun kai samame maboyar masu garkuwar ne a kokarin ceto wata mata da aka sace a yankin Ozuaha
  • Rundunar 'yan sandan ta kwato bindigogi da harsasai, yayin da take ci gaba da farautar wasu daga cikin miyagun da suka tsere

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rivers - Rundunar ’yan sandan jihar Rivers ta bayyana cewa jami’anta sun kashe masu garkuwa da mutane biyu tare da ceto wata mata da aka sace a yankin karamar hukumasr Obio/Akpor na jihar.

Mai magana da yawun rundunar, Grace Iringe-Koko, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a Port Harcourt ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda aka yi wa ɗan majalisar Zamfara ruwan duwatsu da ihun 'ba mu yi'

'Yan sanda sun fafata da masu garkuwa da mutane a Rivers
Jami'an rundunar 'yan sanda na sashen yaki da ta'addanci za su fita aiki. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Masu garkuwa sun budewa ’yan sanda wuta

Jaridar Punch ta rahoto Grace tana cewa jami’an 'yan sanda sun yi nasarar ne bayan kai samame a maboyar masu laifin bisa sahihin bayanan sirri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, masu garkuwan sun budewa jami’an tsaro wuta ne lokacin da suka hango su, lamarin da ya haddasa mummunar musayar wuta tsakaninsu da ’yan sanda.

Kakakin rundunar ta ce jami’an da ke yaki da kungiyoyin asiri na Emohua Annexe ne suka kai farmakin, inda suka gamu da masu garkuwan suna raba kudin fansa da suka karba daga iyalan wacce aka sace.

Ta kara da cewa:

“Sakamakon karfin wutar da ’yan sanda suka yi amfani da ita, masu garkuwa biyu sun mutu, yayin da wasu suka tsere zuwa cikin daji da raunukan harbin bindiga.”

An ceto matar da aka sace

Rundunar ta bayyana cewa an sace matar ne a ranar Jumma’a, 5 ga Disamba, 2025, a kan titin Ozuaha, yankin Emohua. Daga bisani masu laifin sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 1.2, tare da barazanar kashe ta idan ba a biya kudin da wuri ba.

Kara karanta wannan

EFCC ta cafke bokaye da kudin kasashen waje na boge bayan damfarar 'yan Najeriya

Rundunar 'yan sanda ta samu rahoton sace matar ne ta hannun dan uwanta a ranar 9 ga Disamba, 2025, wanda hakan ya sa rundunar ta gaggauta daukar matakin sirri domin ceton ta.

A sanarwar, Grace ta ce jami’an sun samu nasarar ceto matar ba tare da ko da kwarzane ba, tare da kwato wani bangare na kudin fansar da aka riga aka biya.

Jaridar Vanguard ta rahoto sanarwar 'yan sandan na cewa:

“Da misalin karfe 11:30 na safe, jami’anmu sun shiga maboyar masu laifi a cikin daji kusa da titin Ozuaha, inda aka yi artabu mai tsanani kafin aka samu nasarar kashe miyagun.”
An ceto matar da aka yi garkuwa da ita bayan musayar wuta tsakanin masu garkuwa da 'yan sanda a Rivers
Taswirar jihar Rivers, inda 'yan sanda suka kashe masu garkuwa tare da ceto wata mata. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kwato kayayyaki daga hannun 'yan bindiga

Rundunar ta ce an kwato kayayyakin laifi da dama daga wajen, ciki har da, bindigar pump-action guda daya, harsasai biyar, kwankon harsasai biyu, da kuma bindigar dane.

Sanarwar ta kuma ba da tabbacin cewa dukkan kayayyakin suna hannun ’yan sanda yayin da bincike ke ci gaba domin kamo sauran da suka tsere.

Rundunar ’yan sandan Jihar Rivers ta jaddada kudirinta na ci gaba da yakar garkuwa da mutane da fashi da makami.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe basarake, sannan sun sace tsohon jami'in Kwastam

'Yan bindiga sun sace dalibai

A wani labari, mun ruwaito cewa, ‘yan bindiga da ake zargin mambobin kungiyoyin daba ne sun yi awon gaba da dalibai biyar na Jami’ar RSU da ke Emohua a Rivers.

Wani dalibi da ya sha da kyar, ya ce maharan sun afka gidan su ne misalin ƙarfe 2:00 na dare, sannan suka fara harbe mai gadi kafin suka shiga ɗaki-ɗaki suna fitar da dalibai.

Lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan dalibai da ke zaune a kusa da makarantar sun gudanar da zanga-zanga kan yawaitar hare-hare daga kungiyoyin daba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com