Wuta Ta Tashi bayan Fetur Ya Kwarara a Gidaje a Hadarin Tankar Mai

Wuta Ta Tashi bayan Fetur Ya Kwarara a Gidaje a Hadarin Tankar Mai

  • Wani mummunan hadarin tankar man fetur a Edoi ya jikkata mutane da dama tare da lalata dukiyoyi masu darajar daruruwan miliyoyin Naira
  • Shaidun gani da ido sun ce wuta ta bazu ta cikin magudanan ruwa, lamarin da ya haddasa ƙarin matsala a manyan hanyoyi da unguwanni
  • Hukumomi da jami’an tsaro sun shiga lamarin nan take, yayin da Sanata Adams Oshiomhole ya nuna damuwa tare da kiran a ƙara taka-tsantsan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Auchi, Jihar Edo – Mutane da dama sun jikkata, yayin da dukiyoyi masu darajar daruruwan miliyoyin Naira suka lalace sakamakon fashewar tankar mai a garin Auchi a jihar Edo.

Lamarin ya faru ne bayan wata tankar da ke ɗauke da man fetur ta faɗi a kan titin Auchi–Okene, inda man ya zube ya ratsa cikin magudanan ruwa da ramuka a sassa daban-daban na garin.

Kara karanta wannan

Burkina Faso: Sojojin Najeriya da Traore ya tsare na neman daukin gaggawa

Yadda tanka ta yi hadari a Auchi, Edo
Tankar mai da ta kama da wuta a Edo. Hoto: NEMA Nigeria
Source: Facebook

Vanguard ta ce shaidun gani da ido sun ce bayan faɗuwar tankar, wuta ta tashi daga bisani, lamarin da ya haddasa firgici da ruɗani a tsakanin mazauna garin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda tankar mai ta yi hadari a Edo

Rahotanni daga wajen da abin ya faru sun bayyana cewa tankar ta faɗi ne a kan babban titin Auchi–Okene, inda man fetur ya malala cikin magudanan ruwa da ke ratsawa ta cikin gari.

Shaidun gani da ido sun ce daga bisani wuta ta tashi, kuma ta bi magudanan ruwan, lamarin da ya haddasa ƙarin matsala a kan titin Igbe, Warrake kusa da AP, da kuma wasu unguwanni da ke makwabtaka da su.

A cewar rahotanni, yanayin ya sa wutar ta bazu cikin sauri, ta cinye abubuwan hawa, shaguna da gidajen jama'a a yankin.

Tankar mai ta jikkata mutane a Edo

Wani rahoto da hukumar NEMA ta wallafa a X ya nuna cewa sakamakon fashewar tankar man, mutane da dama sun samu raunuka daban-daban.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Gobara ta babbake gidan tsohon gwamnan Zamfara, an tafka asara

An garzaya da wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Auchi domin samun kulawa, yayin da wasu kuma aka kai su asibitocin masu zaman kansu da ke kusa da wurin.

Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, Eno Ikoedem, ta ce hadarin ya auku ne da misalin ƙarfe 6:30 na yamma bayan tankar ta faɗi.

A cewar ’yan sanda, an ɗauki matakan gaggawa domin hana ƙarin asarar rayuka da dukiya, tare da tabbatar da tsaron yankunan da wutar ta shafa.

Hadarin tankar mai a jihar Edo
Jami'an Red Cross wajen aikin ceto a hadarin tankar mai a Edo. Hoto: NEMA Nigeria
Source: Facebook

Sanatan da ke wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya nuna matuƙar damuwa kan lamarin, inda ya buƙaci mazauna yankin da matafiya su ƙara yin taka-tsantsan.

Dalibin jami'a ya yi hadari a Edo

A wani labarin, mun kawo muku cewa wani dalibin jami'ar AAU Ekpoma a jihar Edo ya rasu a hadarin mota da ya rutsa da shi.

Rahotanni sun nuna cewa dalibin ya rasu ne yayin da suke wasa da motoci a murnar kammala karatu a matakin digiri.

Jami'an hukumar FRSC da ke lura da abubuwan hawa sun tabbatar da hadarin da ya jawo mutuwar dalibin a wani sako da ta fitar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng