Gwamnoni Suna Tsaka Mai Wuya, Tinubu Ya Umarce Su kan Kudin Kananan Hukumomi

Gwamnoni Suna Tsaka Mai Wuya, Tinubu Ya Umarce Su kan Kudin Kananan Hukumomi

  • Shugaba Bola Tinubu ya umarci gwamnonin jihohi 36 su bai wa kananan hukumomi kudinsu kai tsaye domin gudanar da ayyuka
  • Tinubu ya ce ba za a samu cikakken ‘yancin kananan hukumomi ba tare da kudaden aiki ba da suke samu kai tsaye
  • Shugaban jam'iyyar APC, Farcesa Nentawe Yilwatda, ya ce jam’iyyar na kara karfi ta hanyar sauya sheka, rijistar mambobi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya umarci gwamnonin jihohi 36 a Najeriya game da kudaden kananan hukumomi.

Tinubu ya bukaci su mika kudaden kananan hukumomi kai tsaye ga domin bin umarnin hukuncin Kotun Koli.

Tinubu ya umarci gwamnoni kudin kananan hukumomi
Taron gwamnonin Najeriya da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Tinubu ya jaddada 'yancin ƙananan hukumomi

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki na kasa na APC karo na 14, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Kungiyar CAN ta yi magana da babbar murya ga Tinubu yayin da ake shirin Kirsimeti

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A gudanar da ganawar a dakin taro na Fadar Shugaban Kasa, Abuja a yau Alhamis 18 ga watan Disambar 2025.

Tinubu ya jaddada cewa ba za a iya samun ‘yancin kananan hukumomi ba idan ba a samar musu da kudaden da za su aiwatar da ayyukansu ba.

Ya ce gwamnatin tarayya za ta tabbatar ba kananan hukumomi kudinsu kai tsaye, wanda hakan cikakken bin umarnin Kotun Koli ne.

Shugaban ya kuma bayyana wa shugabannin APC cewa ya shaida wa Amurka da Tarayyar Turai kudurin kafa ‘yan sandan jiha don magance matsalar tsaro.

A cewarsa, kafa ‘yan sandan jiha zai taimaka wajen karfafa tsaro, musamman a yankunan karkara da ke fuskantar kalubalen ta’addanci.

Shawarar Tinubu ga gwamnoni, shugabannin APC

Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi da shugabannin jam’iyya su kasance masu sassauci da hakuri wajen tafiyar da al’amuran siyasa da mulki.

Ya ce wajibi ne shugabanni su rika sa ido kan abubuwan da ke faruwa a jihohinsu har zuwa matakin kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Bayan shiga APC, Gwamna Fubara ya bayyana shirinsa kan tazarcen Tinubu a 2027

Shugaban ya ce jam’iyyar APC na da rinjaye kuma tana da karfin aiwatar da muhimman sauye-sauye idan aka samu hadin kai.

Ya kuma bukaci jam’iyyar APC ta kara bai wa mata muhimmanci ta hanyar shigar da su cikin manyan tsare-tsaren jam’iyya, cewar TheCable.

Tinubu ya bukaci gwamnoni su bi umarnin kotu kan kuɗin kananan hukumomi
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Karfin da APC ke samu a Najeriya

A jawabinsa, shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yaba da karuwar karbuwa da karfin jam’iyyar a fadin kasa.

Yilwatda ya danganta wannan ci gaba da sauya shekar manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa zuwa APC.

Ya bayyana cewa APC ta kaddamar da rijistar mambobi ta yanar gizo domin kara gaskiya, adalci, da dimokuradiyya a cikin jam’iyyar.

Gwamna ya musanta wawure kudin ƙananan hukumomi

Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Kogi ta ce ana yada jita-jitar karkatar da kudin kananan hukumomi domin bata sunan Gwamna Usman Ododo.

Ma'aikatar yada labarai ta ce kananan hukumomi na karɓar kudinsu kai tsaye, suna aiwatar da ayyuka da kuma biyan albashi da kansu.

Gwamnatin ta ce kananan hukumomin na wallafa ayyukansu don jama'a su tantance, wanda hakan yake karyata zarge-zargen da ake yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.