Kungiyar CAN Ta Yi Magana da Babbar Murya ga Tinubu yayin da Ake Shirin Kirsimeti a Najeiya
- Kungiyar CAN ta nuna matukar damuwa kan karuwar matsalolin rashin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya
- Shugaban CAN a Arewa ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro ta sanya Kiristoci da dama sun sanya shakku kan bukukuwan Kirsimeti
- YakubuPam ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jihohi su tashi tsaye domin kawo karshen matsalar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a Arewa ta yi muhimman kira ga gwamnatin tarayya da kuma gwamnonin jihohi kan matsalar rashin tsaro.
Kungiyar CAN ta bukaci gwamnatin tarayya da na jihohi da su karfafa tsarin tsaro a kasar nan a duk tsawon lokacin bukukuwan Kirsimeti.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta ce shugaban CAN na Arewa, Yakubu Pam, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 18 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CAN ta koka kan rashin tsaro
Yakubu Pam ya ce karuwar rashin tsaro a kasar nan na jefa shakku kan shagulgulan Kirsimeti a al’ummomi da dama a Najeriya.
"Kiristoci da dama suna tunanin za su zauna a inda suke ba tare da yin tafiye-tafiye ba, saboda tsoron lafiyarsu, ganin yadda manyan hanyoyi, yankunan karkara, har ma da wuraren ibada suka zama wuraren da ake kai hare-haren tashin hankali.”
- Yakubu Pam
Shugaban na kungiyar CAN ya ce kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya na ci gaba da kasancewa ginshiki mai muhimmanci ga haɗin kan kasa da zaman lafiyar al’umma.
Wane kira CAN ta yi ga gwamnati?
Yakubu Pam ya jaddada cewa wajibi ne gwamnatin tarayya ta tura jami’an tsaro zuwa yankunan da ke cikin haɗari a lokacin bukukuwan Kirsimeti.
"Yayin da duniya ke shagulgulan wannan lokaci, ina kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnonin jihohin Arewa da Ministan Abuja da su ɗauki matakai cikin gaggawa, domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a lokacin bukukuwan da ma bayan su.”
"Kalubalen tsaro da ke addabar kasar nan a baya-bayan nan, musamman karuwar ayyukan ’yan bindiga, ’yan ta’adda da sauran kungiyoyin masu aikata laifuka a sassa da dama na Arewacin Najeriya, abin damuwa ne matuka.”
- Yakubu Pam
Yakubu Pam ya bayyana cewa Kirsimeti na nuni da bikin haihuwar Yesu Almasihu, wanda a al’ada ake yi da taron iyalai, ibada da ayyukan soyayya da taimako, amma a wannan karon karuwar rashin tsaro na barazana ga wadannan bukukuwa.

Source: Facebook
CAN ba za ta lamunci rashin tsaro ba
"Ba za mu amince da hakan ba a kasar da ke da dimokuraɗiyya, inda ya kamata a kiyaye ’yancin zirga-zirga, ibada da cudanya da jama'a."
"Muna kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi 19 na Arewa da su nuna jajircewa wajen sauke nauyin da ke kansu ta hanyar karfafa tsarin tsaro."
"Inganta ayyukan tattara bayanan sirri, da kuma tura isassun jami’an tsaro zuwa yankunan da ke cikin haɗari, manyan hanyoyi, wuraren ibada da wuraren taruwar jama’a a duk tsawon lokacin bukukuwan Kirsimeti.”
- Yakubu Pam
CAN ta yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi
A wani labarin kuma kun ji cewa kungiyar CAN reshen jihohin Arewa ta nuna alhininta kan rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Kungiyar CAN ta bayyana cewa rasuwar malamin ta bar babban gibi ga harkokin zaman lafiya da tarbiyya, musamman a Arewacin ƙasar.
Hakazalika, kungiyar CAN ta ce Sheikh Dahiru Bauchi ya shafe tsawon rayuwarsa yana ba da gudummawa wajen bunƙasa karatun Alƙur’ani.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


