Wuju Wuju: Abba Kabir Ya Kwarara Yabo ga Tinubu, 'Dan Majalisar APC a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan amincewa da kashe ₦47bn domin aikin titin a jihar
- Abba Kabir ya ce aikin na titin Wuju-Wuju ya fara tun 2013 a zamanin Rabiu Kwankwaso, amma ya tsaya na shekaru takwas
- Ya kuma yabawa Hon. Abubakar Kabir Bichi, yana cewa jajircewarsa a Majalisa ta taimaka wajen samun amincewar aikin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana godiyarsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ayyuka a jihar.
Mai girma Abba Kabir Yusuf ya yi godiyar bisa amincewar gwamnatin tarayya ta kammala aikin titin Wuju-Wuju kan ₦47bn.

Source: Twitter
Tarihin aiki da ake yi tun mulkin Kwankwaso
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron majalisar zartarwa karo na 35, kamar yadda mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanar a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an fara aikin titin ne a shekarar 2013 a zamanin tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, amma aka bar shi ya tsaya na tsawon shekaru takwas.
Gwamna Yusuf ya ce bayan ya hau mulki, gwamnatinsa ta tantance aikin tare da neman sa hannun gwamnatin tarayya domin a kammala shi.

Source: Facebook
Abin alheri da Tinubu ya yi ga Kano
A cewarsa, gwamnatin tarayya ta yi gaggawar amsa bukatar, inda majalisar zartarwa ta kasa ta amince da kashe ₦47bn domin kammala aikin.
Ya bayyana amincewar Shugaba Tinubu a matsayin shaida ta jagoranci nagari da kuma jajircewa wajen bunƙasa ababen more rayuwa a Kano.
Gwamnan ya kuma yabawa Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Bichi, bisa rawar da ya taka wajen samun amincewar aikin.
Ya ce Hon. Bichi mai wakiltar Bichi ya bi diddigin aikin tun daga Majalisa har zuwa fadar shugaban kasa, yana kare muradun Jihar Kano ba tare da gajiya ba.
Gwamna Abba Kabir ya bayyana Bichi a matsayin jakada nagari ga Kano a Majalisa, yana kira ga sauran ‘yan majalisa su koyi jajircewarsa.
Rokon da Abba ya yi ga Tinubu
Har ila yau, ya amince da gudummawar Hon. Bichi a wasu manyan ayyuka, ciki har da cibiyar taro ta kasa da filin wasa na zamani a Bichi.
Gwamnan ya roki Shugaba Tinubu da ya amince da karin manyan ayyuka a Kano, yana mai jaddada cewa ita ce jiha mafi yawan jama’a a Najeriya.
Ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da haɗin gwiwa da tarayya domin samar da ci gaba mai dorewa da amfanin gaske.
Gwamnatin Abba ta sake tura dalibai India
Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi bankwana da dalibai 350 da gwamnatin Kano ta dauki nauyin karatunsu zuwa kasashen waje.
Daliban na daga cikin shirin tura mutane 1,001 karatu ketare da jihar ta kaddamar domin gina hazikan matasa da kuma ba su damar dogaro da kansu.
Gwamnan ya shawarci daliban su zama jakadu nagari na Kano da Najeriya tare da aiki da ilimin da za su samu ga ci gaban jiharsu da kuma iyalansu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

