Dalung Ya Lissafo Matsaloli 4 da Cire Tallafin Mai da Tinubu Ya Yi Ya Jawo a Najeriya

Dalung Ya Lissafo Matsaloli 4 da Cire Tallafin Mai da Tinubu Ya Yi Ya Jawo a Najeriya

  • Tsohon Ministan wasanni da matasa, Solomom Dalung ya fadi illar cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi
  • Solomon Dalung ya soki yadda gwamnati ta kasa sauya rayuwar 'yan Najeriya duk da cire tallafin man fetur din da aka yi
  • Tsohon Ministan ya bayyana cewa cire tallafin man fetur ya jawo 'yan Najeriya sun tsinci kansu cikin wahala

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon Ministan wasanni da matasa, Solomon Dalung, ya sake sukar Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan cire tallafin man fetur.

Solomon Dalung ya ce cire tallafin man fetur bai kawo saukin da ake tsammani ba, sai dai ya haifar da talauci, yunwa, hauhawar farashi da kuma karuwar matsalar rashin tsaro.

Solomon Dalung ya ragargaji Shugaba Bola Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Solomon Dalung Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Barr Solomon Dalung
Source: Facebook

Solomon Dalung ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin 'Sunrise Daily' na tashar Channels tv a ranar Alhamis, 18 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Akwai damuwa: An yi hasashen Tinubu zai iya neman hanyar dauwama a mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya cire tallafin man fetur

A lokacin rantsar da shi a watan Mayun 2023, Shugaba Tinubu ya sanar da kawo karshen tallafin mai.

Shugaban kasar ya ci gaba da jaddada cewa wannan mataki ya zama dole domin ceto tattalin arzikin kasa daga rushewa gaba ɗaya, tare da cewa hakan ya ’yantar da kuɗaɗen da ake raba wa jihohi.

Me Dalung ya ce kan cire tallafin fetur?

Sai dai yayin hirar, Solomon Dalung ya ce cire tallafin bai kawo alherin komao ba, illa bala’o’i.

"Tabbas an cire tallafin, yadda aka yi shi ya sake nuna cewa shugaban kasa a wancan lokaci bai fahimci yadda gwamnati ke aiki ba da kuma rudanin kasa kamar Najeriya ba."
“Ya kamata a yi shawarwari. A wancan lokaci babu cikakkiyar gwamnati. Shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa ne kawai aka rantsar, kuma hakan ba gwamnati ba ce."
"Ya kamata a samu cikakkiyar gwamnati mai majalisar ministoci, masu ba da shawara da masu tsara manufofi kafin a yanke irin wannan shawara, amma hakan bai faru ba."

Kara karanta wannan

An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

“Mutum ɗaya ne kawai ya faɗa, ’yan Najeriya suka karɓa da fatan wani alheri zai biyo baya. Bayan shekaru, babu abin da ya fito sai talauci, yunwa, hauhawar farashi da rashin tsaro.”

- Solomon Dalung

Solomon Dalung ya soki cire tallafin man fetur
Tsohon Ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung Hoto: Barr Solomon Dalung
Source: Facebook

Dalung ya zargi gwamnatin Tinubu

Tsohon Ministan ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da rashin bayyana yadda aka tafiyar da cire tallafin, yana mai cewa ya kamata ’yan Najeriya sun fi jin daɗin rayuwa tun bayan aiwatar da matakin.

“Tun da an cire tallafin gaba ɗaya, ya kamata ’yan Najeriya su kasance suna rayuwa fiye da mutanen Dubai, idan aka yi la’akari da dimbin kuɗaɗen shiga da suka shiga aljihun gwamnati."

- Solomon Dalung

Dalung ya soki gwamnonin Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan wasanni da matasa, Solomon Dalung, ya ragargaji gwamonin jihohin Arewa.

Solomon Dalung ya yi zazzafar suka inda ya kira gwamnonin marasa imani, marasa tsoron Allah kuma azzalumai bayan sun ce Shugaba Bola Tinubu ya cika alkawuran da ya daukarwa Arewa.

Tsohon ministan ya bayyana mamakinsa kan yadda gwamnonin Arewa ke ikirarin cewa komai na tafiya lafiya a yankin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng