Mataimakin Kwamishinan Ƴan Sanda Ya Yanke Jiki Ya Faɗi, Ya Mutu Ana tsakiyar Taro

Mataimakin Kwamishinan Ƴan Sanda Ya Yanke Jiki Ya Faɗi, Ya Mutu Ana tsakiyar Taro

  • Wani babban jami’in ‘yan sanda, ACP Ogbon-Inu Taiwo Popoola, ya rasu yayin da ake gudanar da muhimmin taro a Abakaliki, jihar Ebonyi
  • An ce jami'in ya yanke jiki ya fadi lokacin da ake taron a ofishin kwamishinan ‘yan sanda, inda ya ce 'ga garinku nan' bayan zuwa asibiti
  • Yayin da rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta tabbatar da mutuwar jami'in, wasu majiyoyi sun fito da bayanai game da silar mutuwarsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ebonyi - Wani mataimakin kwamishinan yan sanda (ACP) Ogbon-Inu Taiwo Popoola, ya yanke jiki ya fadi, ya mutu yayin da yake bakin aiki a jihar Ebonyi.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar Talata, a lokacin wani taron manyan jami’an runduna da ake gudanarwa a ofishin kwamishinan ‘yan sanda na jihar da ke Abakaliki.

Kara karanta wannan

Ba a gama murnar cin zabe ba, yan ta'adda sun sace mataimakin ciyaman da kansiloli 2

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda ya mutu yayin da ake taro a Ebonyi.
Sufeta Janar Kayode Egbetokun ya jagoranci taron manyan jami'an 'yan sanda a Abuja. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda ya mutu

Kafin rasuwarsa, mataimakin kwamishinan 'yan sanda ya kasance jami’in da ke kula da sashen leken asiri na jihar (SID), kamar yadda fitaccen mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama, ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun ce yayin da ake tsaka da taron, marigayin ya fara fuskantar matsanancin rashin numfashi, inda aka lura yana shakar iska da kyar, har dai ya yanke jiki ya fadi.

Bayan ya suma ne aka garzaya da ACP Popoola zuwa cibiyar kula da lafiyar ‘yan sanda (PMC) da ke hedkwatar rundunar a Abakaliki.

Rahotanni sun ce likitocin rundunar sun yi iya kokarinsu domin farfado da shi, amma abu ya ci tura, wanda a karshe likitocin suka tabbatar da rasuwarsa.

Hasashe kan silar mutuwar dan sandan

Majiyoyi sun bayyana cewa binciken farko na likitoci ya nuna cewa mutuwar ta samo asali ne daga bugun zuciya, wanda ya faru sakamakon cutar hawan jini da ya ke fama da ita.

Kara karanta wannan

Kakakin Majalisa na neman haddasa rigima a jam'iyyar APC kan tikitin zaben 2027

Bayan rasuwarsa, an ajiye gawar mataimakin kwamishinan 'yan sandan a dakin ajiyar gangar jikin na asibitin koyarwa na jami'ar tarayya ta Alex Ekwueme (AE-FUTHA 1) da ke Abakaliki.

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana marigayi ACP Popoola a matsayin jami’i mai kwazo, kwarewa da jajircewa wajen aiki, wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin hidimar kasa.

An ce mataimakin kwamishinan 'yan sandan ba ya fama da wata matsalar rashin lafiya kafin mutuwarsa
Taswirar jihar Ebonyi, inda mataimakin kwamishinan 'yan sanda ya mutu ana tsakiyar taro. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da lamarin

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi, Joshua Ukandu, ya tabbatar da rasuwar babban jami'in dan sandan a ranar Alhamis, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Joshua Ukandu ya ce:

“Eh, daya daga cikin jami’anmu ya samu matsala yayin taro, aka gaggauta kai shi asibiti, amma abin takaici, ba a samu damar farfado da shi ba.”

Ya kara da cewa lafiyar marigayin kalau, kuma ba ya fama da wata rashin lafiya kafin faruwar lamarin, yana mai cewa da yana fama da rashin lafiya, da bai halarci taron ba.

ACP na 'yan sanda ya mutu a Sokoto

A wani labari, mun ruwaito cewa, rundunar ‘yan sanda ta sanar da rasuwar mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka, DCP Kabir Abdu.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun hargitsa gari, sun kora mutane daji a Zamfara

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa an kwantar da marigayin wanda ke aiki a Sokoto a asibiti tun ranar 12 ga Disamba, 2025, kafin rasuwarsa bayan jinya mai tsawo.

Kwamishinan ‘yan sandan Sokoto, CP Ahmed Musa, wanda ya yi ta'aziyya, ya bayyana mamacin a matsayin jajirtaccen jami’i mai ladabi, kwarewa da sadaukarwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com