Kotu Ta Gindaya Sharudda Masu Tsauri kafin Sakin Ministan Buhari, Ngige

Kotu Ta Gindaya Sharudda Masu Tsauri kafin Sakin Ministan Buhari, Ngige

  • Tsohon ministan kwadago, Dr. Chris Ngige ya samu nasara a bukatar belin da ya shigar gaban babbar kotun Abuja
  • Mai Shari'a Maryam Hassan ta amince Ngige ya ci gaba da zama a belin wucin gadi da EFCC ta ba shi, ta gindaya sharudda masu tsauri
  • Ngige na fuskantar shari'a ne kan zargin amfani da ofishinsa na minista a mulkin Buhari wajen bai wa kamfanoninsa kwangiloli

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Gwarinpa a Abuja, a ranar Alhamis, ta amince da bukatar belin tsohon Ministan Kwadago, Sanata Chris Ngige.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi watsi da bukatar Malami, EFCC za ta ci gaba da tsare tsohon minista

Kotun ta amince Ngige ya ci gaba da kasancewa a kan belin wucin-gadi da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta ba shi a baya.

Dr. Chris Ngige.
Ministan kwadago da samarda ayyukan yi a gwamnatin Muhammadu Buhari, Dr. Chris Ngige Hoto: Chris Ngige
Source: Twitter

Mai shari’a Maryam Hassan ce ta yanke wannan hukunci yayin da take sauraron buƙatar beli da lauyan Ngige, Patrick Ikwueto (SAN), ya gabatar, kamar yadda Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sharuddan da kotu ta kafa wa Ngige

A cikin hukuncinta, Mai shari’ar ta umarci Ngige da ya gabatar da mutum daya da zai tsaya masa, wanda dole ya kasance darakta da ke bakin aiki a Gwamnatin Tarayya.

Haka zalika, kotun ta shaida wa tsohon ministan cewa dole duk daraktan da zai tsaya masa ya kasance ya mallakin fili ko gida.

Mai shari’a Maryam Hassan ta kuma bayar da umarnin cewa duk wanda zai tsaya wa Ngige, ya ajiye takardun mallakar kadararsa tare da takardun tafiye-tafiye watau fasfo a gaban kotu.

Ta bayyana cewa ba za a maida masa wadannan takardu ba har sai Ngige ya gano fasfonsa da aka sace ko kuma ya yi wani sabo.

Wane beli EFCC ta bai wa tsohon minista?

Kara karanta wannan

Tattaunawar Buhari da Lai Mohammed a kan toshe amfani da Twitter a Najeriya a 2021

Tun da farko dai, EFCC ta bai wa Ngige beli saboda kasancewarsa wanda aka sani, inda ta umarce shi da ya miƙa fasfo tare da gabatar da mutum ɗaya da zai tsaya masa.

Yayin da yake adawa da buƙatar belin, Sylvanus Tahir, lauyan EFCC, ya shaida wa kotu cewa Ngige ya gaza gabatar da fasfo ɗin tun bayan dawowarsa Najeriya a ranar 19 ga Nuwamba, 2025.

Hukumar EFCC.
Allon sanarwa da ke kuA da babban ofishin hukumar EFCC ta kasa da ke Abuja Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

Da yake mayar da martani, Patrick Ikwueto, lauyan Ngige, ya ce wanda yake karewa ya rubuta wa EFCC wasika bayan dawowarsa, inda ya sanar cewa an yi masa fashi a Landan kuma an sace masa muhimman abubuwa, ciki har da fasfo.

Sai dai duk da korafin lauyan EFCC, kotun ta amince Ngige ya ci gaba da zama a belin wucin gadi, tare da kafa sharudda, kamar yadda The Cable ta kawo.

Kotu ta hana belin Abubakar Malami

A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi fatali da bukatar ba da beli da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami ya gabatar a gabanta.

A hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, Mai shari’a Babangida Hassan, ya bayyana cewa EFCC na ci gaba da tsare Malami ne bisa umarnin kotu.

Kara karanta wannan

Bayan suka ta ko ina, an dakatar da yi wa dogarin Shugaba Tinubu karin girma

Alkalin ya ce bukatar da Malami ya gabatar tana da matsala ta fuskar doka, domin tana neman kotu ta soke ko ta yi nazarin hukuncin wata kotu da ke fa hurumi irin nata.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262