Tinubu Ya ba Shugaba Traore na Burkina Faso Hakuri kan Abin da Ya Faru
- Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya isar da sako daga Bola Tinubu zuwa Shugaban Burkina Faso
- Kasashen na Afrika biyu sun tattauna kan tsaro, yaki da ta’addanci, da karfafa hadin gwiwar yankin Sahel
- Najeriya ta bayyana nadama kan matsalar jirgin sama da ya sauka gaggawa a Burkina Faso tare da jaddada girmama ikon kasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ouagadougou, Burkina Faso - Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya isar da sakon Bola Tinubu a Burkina Faso.
Tuggar ya isar da sakon hadin kai da zumunci daga Bola Tinubu zuwa Shugaban Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré.

Source: Facebook
Tsaro: Najeriya ta tattauna da Burkina Faso
Legit Hausa ta samu rahoton ne daga shafin ma'aikatar harkokin kasashen waje da aka wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tuggar ya mika sakon ne yayin wata ganawa ta musamman da Shugaba Traoré a Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso.
A yayin ganawar, kasashen biyu sun tattauna hanyoyin karfafa hadin gwiwa a fannoni daban-daban, musamman a bangaren tsaro da yaki da ta’addanci a yankin.
Da yake magana bayan ganawar, Tuggar ya ce Najeriya da Burkina Faso suna da dadaddiyar alaka tare da kalubalen tsaro iri daya, inda ya ce ganawar na da nufin kara fahimta da kyautata zumuncin makwabta.
“Mun yi musayar ra’ayoyi kan hadin gwiwa a fannoni da dama. Mun kuma tattauna batun jirgin saman Najeriya da ya yi saukar gaggawa a Burkina Faso.”
- In ji Tuggar.

Source: Twitter
Nadamar Najeriya kan lamarin Burkina Faso
Ministan ya amince cewa an samu kura-kurai na tsari wajen ba da izinin shigar jirgin cikin sararin samaniyar Burkina Faso, inda ya bayyana nadamar Najeriya kan faruwar lamarin.
Sai dai ya jaddada cewa Najeriya na girmama cikakken ikon Burkina Faso da ka’idojin sufurin jiragen sama na kasa da kasa, cewar Zagazola Makama.
Tuggar ya kuma nisanta gwamnatin tarayya daga kalaman da wani jami’in jam’iyyar siyasa a Najeriya ya yi, wanda ya zargi Burkina Faso da cin zarafin sojojin Najeriya.
Yusuf Tuggar ya ce:
“Mun bayyana karara cewa ba mu da alaka da wadannan kalamai, kuma muna mika cikakkiyar nadama ga gwamnatin Burkina Faso.”
Ministan ya yaba wa Shugaba Traoré da gwamnatinsa kan nuna zumunci da kyakkyawar mu’amala da sojojin a jirgin saman yayin zamansu a Burkina Faso.
Ya kara da cewa tattaunawar ta shafi kokarin yankin wajen yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi, inda ya ce Burkina Faso ta samu nasarori a ayyukan dakile ta’addanci.
Tuggar ya tabbatar da kudirin Najeriya na ci gaba da tattaunawa, karfafa hadin kai a yankin, da kuma zurfafa hadin gwiwa da Burkina Faso da sauran kasashen yankin domin tunkarar kalubalen tsaro da suka shafi kowa.
Shugaban Burkina Faso ya soki sojojin Najeriya
Kun ji cewa majiyoyi sun nuna cewa Burkina Faso ta saki wasu jami’an sojojin saman Najeriya bayan tattaunawa tsakanin kasashen biyu.
Tawagar Najeriya karkashin jagorancin Ministan harkokin waje ta gana da shugabannin Burkina Faso domin warware batun cikin lumana.
Biyo bayan lamarin, masu ruwa da tsaki sun bayyana matakin a matsayin nasarar diflomasiyya da ke karfafa hadin kai a yankin Sahel.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


