Labarin Tsohon Sakataren Buhari da Ministoci da Mukarraban Gwamnati Ke Shakka

Labarin Tsohon Sakataren Buhari da Ministoci da Mukarraban Gwamnati Ke Shakka

  • 'Yar marigayi tsohon shugaban kasa, Fatima Buhari ta yi magana kan tasirin da daya daga cikin na kusa da mahaifinta yake da shi
  • Fatima ta ce Tunde Sabiu yana da karfin iko a fadar shugaban kasa ta hanyar sarrafa takardu da samun ganawa da Buhari
  • Ta bayyana cewa ministoci da dama sun ji tsoron bata masa rai, suna ganin ba za a iya cimma komai a gwamnati ba tare da shi ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Yar marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta yi magana game da mulkin mahaifinta na biyu a karkashin mulkin farar hula.

Fatima Buhari, daya daga cikin manyan 'ya 'yan marigayi Buhari, ta ce Tunde Sabiu, tsohon sakataren na musamman ga mahaifinta yana da karfi.

Yadda tsohon sakataren Buhari ya sheka ayarsa a fadar shugaban kasa
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Tunde Sabiu. Hoto: Buhari Sallau.
Source: Facebook

Yadda mukarraban gwamnati ke shakkar sakataren Buhari

Kara karanta wannan

"A bar shi ya huta": Nasir El Rufa'i ya yi magana game da littafi kan Buhari

Fatima ta bayyana hakan ne a cikin littafin tarihin Buhari mai taken 'From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari', wanda Charles Omole ya rubuta, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fatima ta ce Sabiu da ke kusa da tsohon shugaban kasa, yana da iko mai karfi fiye da matsayinsa a hukumance.

Ta ce ba jita-jita take yadawa ba, sai dai abin da ta gani da idonta kuma ta ji da kunnenta a lokacin da mahaifinta ke rike da shugabancin Najeriya.

A cewarta, labarai game da karfin ikon Tunde Sabiu sun yadu sosai a lokacin, har wani bako daga kasashen waje ya yi barkwanci cewa ba za a iya ganin shugaban kasa Buhari ba sai da yardar Sabiu.

Fatima ta kara da cewa wasu ministoci sun rika nuna kamar Sabiu ne kadai ke iya taimakawa wajen tafiyar da muhimman al’amuran gwamnati.

Ta ce akwai fargaba a gwamnatin cewa duk wanda ya bata wa Sabiu rai, aikinsa na iya tsaya wa cik ko kuma a dakatar da shi gaba daya.

“Tunde, “yana da cikakken iko a kan mafi yawan ministoci."

Kara karanta wannan

Abin da ya sa ake ganin ya kamata a daure kusan duka ministocin Buhari a gidan yari

- Fatima Buhari

An bayyana karfin ikon wani sakataren Buhari a fadar shugaban kasa
Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Hoto: Garba Shehu.
Source: Facebook

Fatima ta fadi tasirin tsohon sakataren Buhari

Fatima ta ce ya bayyana musu karara cewa ba za su iya yin komai ba tare da shigarsa cikin lamarin ba.

Ta bayyana cewa ko da yake matsayin sakataren na musamman yake, yana da ikon sarrafa hanyoyin ganin shugaban kasa, hakan na iya janyo wuce gona da iri.

“Ya kasance mai karfi sosai, amma wani lokaci a gabana, Baba ya taba yi wa Tunde tsawa."

Ta ce wannan lamari abu ne da ba kasafai Buhari ke yi ba, kasancewarsa mutum ne da ya fi son lallashi da nasiha fiye da tsawa.

Ta kuma bayyana damuwa kan zargin sa hannun Buhari a takardu ba tare da saninsa ba a lokacin mulkinsa, cewar rahoton Punch.

Fatima, wacce kwararriyar mai binciken kudi ce ta ce gano wasu takardu tare da nuna wa mahaifinta misalan sa hannun bogi da aka yi da sunansa.

'An dakile ni a mulkin Buhari' - Monguno

Kara karanta wannan

Bayan rasuwarsa, Aisha ta fadi kuskuren Buhari cikin mulkinsa na shekara 8

A wani labarin, tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan lamuran tsaro ya bayyana matsalar da aka samu a mulkin Muhammadu Buhari.

Babagana Monguno ya ce wasu miyagu a fadar shugaban kasa sun raunana aikinsa a zamanin mulkin marigayi Buhari.

Ya bayyana cewa rikici kan sauya kamfanin da ke samar da mai ga jiragen shugaban kasa ya bankado wasu sirruka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.