An Fara Raba N200,000 da Buhun Shinkafa ga Kowane Mutum 1 da Ya Shiga Shirin RHIESS

An Fara Raba N200,000 da Buhun Shinkafa ga Kowane Mutum 1 da Ya Shiga Shirin RHIESS

  • Gwamnatin tarayya ta fara raba wa tsofaffin mutane 250 tallafin kudi, abinci da kiwon lafiya kyauta domin taimaka wa rayuwarsu a Delta
  • Uwargidar gwamnan Delta, Deaconess Tobore Oborevwori ta tabbatar da cewa tallafin ya fito ne daga ofishin matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu
  • Kowane tsoho daga cikin mutane 250 da aka zakulo a fadin jihar Delta ya samu tallafin N200,000, buhun shinkafa da kula da lafiya kyauta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta gwangwaje wasu tsofaffi su 250 da tallafin makudan kudi, buhunan shinkafa da kiwon lafiya kyauta.

Kara karanta wannan

NLC: Ajaero ya fadi sabon alkawarin da Tinubu ya dauka game da rashin tsaro

Gwamnatin ta raba wannan kayan arziki ne ta hannu ofishin uwargidar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, wacce matar gwamnan Delta ta wakilce ta a wurin kaddamar da shirin.

Uwargidar gwamnan Delta, Oborevwori.
Uwargidar gwamnan Delta, Deaconess Tobore Oborevwori a taron kaddamar da tallafin tsofaffi Hoto: Ovie Success
Source: Facebook

An fara rabawa tsofaffi tallafin N200,000

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kowane mutum daya daga cikin dattawa 250 ya samu tallafin N200,000, buhun shinkafa da katin shaidar kula da lafiya kyauta a Delta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya sa gwamnatin ta kashe jimillar Naira biliyan 1.9 domin tallafawa dattawan da shekarunsu suka ja, ƙarƙashin Kwamitin Gudanarwa na shirin Renewed Hope Initiative (RHI).

An raba tallafin ne a yayin zagaye na uku na Renewed Hope Initiative Elderly Support Scheme (RHIESS), wanda aka gudanar ranar Talata a birnin Asaba, mai taken “Farin Cikin Tsofaffin Mutane.”

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta samu wakilcin Matar Gwamnan Jihar Delta, Deaconess Tobore Oborevwori a wurin wannan taro, in ji jaridar Punch.

Jawabin matar Tinubu kan taimakon tsofaffi

A jawabin da aka gabatar a madadinta, Oluremi ta bayyana shirin agaza wa tsofaffi a matsayin aikin jin ƙai da nufin tabbatar da ’yan Najeriya da suka tsufa suna rayuwa cikin mutunci, farin ciki da jin cewa ana kula da su.

Kara karanta wannan

Shugaban ƙaramar hukuma ya kinkimo aiki, zai kashe Naira biliyan 11 a wata 12

“Wannan shirin jin ƙai yana nuna ƙoƙarinmu na tabbatar da cewa tsofaffin ’yan ƙasa suna rayuwa cikin mutunci da farin ciki, a ƙasa da ke nuna kulawa ta gaskiya ga jama’arta,” in ji ta.

Ta ce tun bayan kafa gwamnati a 2023, shirin RHI ya zama al’ada a duk watan Disamba na kowace shekara, ana taimakawa tsofaffi domin yaba gudunmawar da suka bayar wajen gina ƙasa.

A cewarta, shirin yana tallafa wa gajiyayyun tsofaffi 250, masu shekaru 65 zuwa sama, a kowace jiha cikin jihohi 36, da Babban Birnin Tarayya.

Oluremi Tinubu.
Uwargidar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu tana jawabi a taro Hoto: Oluremi Tinubu
Source: Facebook

Oluremi Tinubu ta ce shirin ya hada har da tsofaffin mata da matan jami’an tsaro na ƙungiyar DEPOWA, tana mai cewa jimillar wadanda ke amfana ya kai 9,500 a faɗin ƙasar nan.

A nata jawabin ta bakin wakiliyarta, Mrs. Josephine Emu, uwargidar gwamnan Delta, Deaconess Tobore Oborevwori, ta yi godiya ga Matar Shugaban Ƙasa bisa wannan tallafi da ya kawo sauƙi ga rayuwar tsofaffin jihar.

Gwamna ya fara ba zawarawa alawus

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya kaddamar da shirin tallafawa zawarawa, inda mata 10,000 za su amfana da tallafi duk wata.

Kara karanta wannan

An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

Gwamnan ya ce wannan matakin wani bangare ne na alkawuran da ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓe na kafa gwamnatin da za ta jawo kowa a jikinta.

Gwamna Oborevwori ya bayyana cewa, a karkashin shirin, kowace bazawara za ta rika karɓar tallafin kuɗi na ₦15,000 a kowane wata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262