Gwamnatin Tarayya Ta Binciko Gaskiya, Ta Kori Manyan Jami'ai 38 daga Aiki a NSCDC
- Wani da ya kai matsayin Mataimakin kwamanda da wasu manyan jami'an NSCDC sun rasa aikinsu bayan gano laifuffukan da suka aikata
- Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar CDCFIB ta sallami manyan jami'ai 38 daga aiki, tare da wasu kananan ma'aikata 20 a shekarar 2025
- Kwamandan NSCDC na kasa, Ahmed Audi ya bukaci jami’ai da ma’aikatan hukumar da su kasance masu mai da hankali, ladabi da ƙwarewa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta kori manyan jami'ai 37 da wani mataimakin babban kwamanda (ACG) na hukumar tsaron rayukan al'umma ta NSCDC.
An kori ACG tare da wasu manyan jami’ai 37 saboda rashin biyayya da kuma halayen da ba su dace da manyan jami’ai ba, kamar yadda Dokokin Aikin Gwamnati (PSR) suka tanada.

Source: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa mai magana da yawun hukumar NSCDC ta kasa, Babawale Afolabi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Laraba.
Hukumar NSCDC ta kori jami'ai sama da 70
A cewarsa, jimillar jami’ai 76, manya da ƙanana ne aka ɗauki matakan ladabtarwa a kansu a shekarar 2025 bisa laifuffuka daban-daban da aka gano sun aikata.
Kakakin NSCDC ya ce jami'an da aka hukunta sun aikata laifuffuka kamar rashin biyayya, canza wurin aiki ba bisa ƙa’ida ba, karɓar rashawa, da wasu ayyuka da suka saɓa wa ƙimomi da ɗabi’un aikin hukumar.
Afolabi ya ambato Kwamandan NSCDC na kasa, Ahmed Audi, na cewa sun dauki mataki ne bayan shawarwarin Hukumar CDCFIB da kuma kwamitocin ladabtarwa na manyan da ƙananan ma’aikatan NSCDC.

Kara karanta wannan
Shugaban Ƙasa, gwamnoni da ciyamomi sun raba Naira tiriliyan 1.92 a watan Nuwamba
Dalilan korar manyan jami'an NSCDC 38
Jami'in ya bayyana cewa an sallami manya 38 daga aiki gaba ɗaya bisa aikata manyan laifuffuka, rashin biyayya da kuma halayen da ba su dace da matsayinsu ba, kamar yadda Dokokin Aikin Gwamnati suka tanada.
Bugu da ƙari, an rage mukamin manyan jami’ai biyu da matakai biyu, an rage wa wani jami’i matsayi da mataki ɗaya tare da cire masa fifikon dadewa a aiki, yayin da aka bai wa jami’ai biyar wasiƙun gargaɗi.
“Bayan kammala zaman Kwamitin Ladabtarwa na Ƙananan Ma’aikata, an sallami ma’aikata 20 daga aiki, an rage wa ma’aikata uku matsayi da mataki ɗaya, yayin da aka bai wa ma’aikata bakwai wasiƙun gargaɗi,” in ji sanarwar.

Source: Twitter
NSCDC ta ce waɗannan matakai na ladabtarwa na daga cikin gyare-gyaren da ake ci gaba da aiwatarwa domin tsarkake hukumar da kuma ƙarfafa amincewar jama’a ga ayyukanta.
Kwamandan NSCDC ya yi kira ga jami’ai da ma’aikatan hukumar da su kasance masu mai da hankali, ladabi da ƙwarewa wajen aiwatar da ayyukansu na doka, in ji The Nation.
NAHCON za ta dauki ma'aikata
A wani labarin, kun ji cewa hukumar NAHCON ta bude shafin daukar ma'aikatan lafiya da za su shiga tawagarta a lokacin aikin hajjin shekara mai zuwa.
NAHCON ta gayyaci ma’aikatan lafiya da ke sha’awar wannan aiki da su shiga shafin intanet da ta tanada domin cike fam din neman aikin na 2026.
Ta kara da cewa duk wadanda za su nemi aikin dole su kasance ma'aikata, sannan kuma ba su yi irin wannan aiki ba a ayyukan Hajji uku.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

