Burkina Faso: Shugaba Traore Ya Saki Sojojin Najeriya bayan Ganawa da Tuggar

Burkina Faso: Shugaba Traore Ya Saki Sojojin Najeriya bayan Ganawa da Tuggar

  • Rahoto ya nuna cewa Burkina Faso ta saki wasu jami’an sojin saman Najeriya bayan tattaunawa mai zurfi tsakanin kasashen biyu
  • Tawagar Najeriya karkashin jagorancin Ministan harkokin waje ta gana da shugabannin Burkina Faso domin warware batun cikin lumana
  • Biyo bayan lamarin, masu ruwa da tsaki sun bayyana matakin a matsayin nasarar diflomasiyya da ke karfafa hadin kai a yankin Sahel

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Burkina Faso ta saki jami’an sojin saman Najeriya 11 bayan shafe kwanaki tara suna tsare, biyo bayan tattaunawar diflomasiyya mai zurfi da gwamnatin tarayyar Najeriya ta jagoranta.

Sakin jami’an ya zo ne jim kadan bayan kammala ziyarar wata tawagar Najeriya a birnin Ouagadougou, wacce ta gudanar da tattaunawa da manyan jami’an Burkina Faso ciki har da shugaban kasa, Ibrahim Traoré.

Kara karanta wannan

Burkina Faso: Sojojin Najeriya da Traore ya tsare na neman daukin gaggawa

Tawagar Najeriya a kasar Burkina Faso
Wakilan Najeriya da shugaban Burkina Faso. Hoto: Zagazola Makama|Nigerian Affairs Journal
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa matakin ya kawo karshen lamarin da ya ja hankalin masu lura da harkokin tsaro a yankin, tare da bude sabon babi na fahimta da jituwa tsakanin kasashen biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An saki sojojin Najeriya a Burkina Faso

Tawagar da ta wakilci Najeriya ta kunshi manyan jami’ai daga ma’aikatar harkokin waje, ma’aikatar tsaro da kuma hedikwatar rundunar sojin saman Najeriya.

An ba tawagar wannan aiki ne domin neman mafita ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna, ba tare da dagula alaka ko kara tsamin dangantaka ba.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa manufar ziyarar ita ce kwantar da hankula da kuma tabbatar da sakin jami’an da aka tsare ta hanyar lumana.

An yi aiki da diflomasiyya a Burkina Faso

A cewar majiyar, wannan mataki ya nuna yadda Najeriya ke fifita diflomasiyya da kyakkyawar mu’amala da makwabta wajen warware matsaloli masu sarkakiya.

Kara karanta wannan

Wasu manya a Kano sun ajiye Abba a gefe, sun ce Barau suke so a 2027

Majiyar ta ce ziyarar ta mayar da hankali kan nauyin da kasashen ke da shi na bai daya wajen tinkarar kalubalen tsaro a yankin Sahel.

Haka kuma, tawagar ta jaddada kudirin Najeriya na bin ka’idojin kasa da kasa a harkokin sufurin jiragen sama da ayyukan soja.

Alakar Najeriya da kasar Burkina Faso

Rahotanni sun nuna cewa Najeriya da Burkina Faso sun dade suna aiki tare a fannoni da dama na tsaro, ciki har da horaswa, musayar bayanan sirri da yunkurin wanzar da zaman lafiya a yankin Yammacin Afirka.

Kasashen biyu, tare da sauran mambobin kungiyar Sahel, sun sha haduwa wajen yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi da ke barazana ga zaman lafiyar yankin.

Ministan Najeriya na magana a Burkina Faso
Yusuf Tuggar yayin jawabi a Burkina Faso. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Tribune ta rahoto cewa tawagar Najeriya ta yi amfani da damar wajen tuna wa hukumomin Burkina Faso irin wannan doguwar alakar hadin kai da ke tsakaninsu.

Martanin Najeriya da Burkina Faso

Jami’ai daga bangarorin biyu sun nuna kwarin gwiwa cewa warware wannan lamari cikin nasara zai kara zurfafa fahimta da amana a tsakanin kasashen.

Sun bayyana cewa wannan nasara za ta taimaka wajen karfafa hadin gwiwar tsaro da kokarin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Kara karanta wannan

'Za a kamo shi,' Benin ta gano kasar da sojan da ya so juyin mulki ya buya

Sojojin saman Najeriya sun nemi dauki

A wani labarin, kun ji cewa kafin sakin sojojin Najeriya da aka rike a Burkina Faso, dakarun sun nemi a kai musu dauki.

A korafin da suka yi, sun koka da cewa suna fargabar cewa za su iya yin bikin Kirsimeti a tsare a kasar Burkina Faso.

Sai dai tun a lokacin, ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce tana kokari wajen ganin sun dawo gida kafin Kirsimeti.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng