Shugaban Hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed da Takwaransa na NUPRC Sun Yi Murabus
- Shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed da takwaransa na hukumar NUPRC, Gbenga Komolafe sun yi murabus daga kan mukamansu
- Hakan na zuwa ne bayan shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya zargi Farouk Lawal da wadaka da kudi fiye da abin da yake samu
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura sunayen mutum biyu da za su maye gurbinsu ga Majalisar Dattawa domin tabbatar da nadinsu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Kasa (NMDPRA), Farouk Ahmed ya yi murabus daga mukaminsa yau Laraba, 17 ga watan Disamba, 2025.
Wannan na zuwa ne bayan shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Aliko Dangote ya yi zargin cewa shugaban hukumar NMDPRA na biya wa ƴaƴansa guda huɗu kuɗin makaranta a Switzerland da suka kai dala miliyan 5.

Source: Facebook
Farouk Ahmed ya yi murabus
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da murabus din Farouk Ahmed a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika, shugaban hukumar NUPRC, wacce ita ma ta shafi kula da harkokin man fetur, Gbenga Komolafe ya yi murabus daga mukaminsa nan take.
Onanuga ya ce Shugaba Bola Tinubu ya tura sunayen mutane biyu zuwa Majalisar Dattawa domin maye gurbinsu.
Shugaba Tinubu ya maye gurbinsu
Shugaban kasar ya rubuta wasika zuwa Majalisar Dattawa, yana rokon a gaggauta tantancewa da amincewa da Oritsemeyiwa Eyesan a matsayin shugaban NUPRC, da kuma Saidu Mohammed a matsayin shugaban NMDPRA.
Sanarwar ta ce, "Wadanda aka nada guda biyu kwararru ne a fannin harkokin mai da iskar gas."
Sa'o'i kafin murabus dinsa, tsohon shugaban NMDPRA ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya, Abuja.
Tinubu ya gana da tsohon shugaban NMDPRA
Sanye da kayan gargajiya, Farouk Ahmed ya shafe kasa da mintuna 30 yana ganawa da Bola Tinubu kafin ya bar harabar Aso Rock.
Babu wata sanarwa a hukumance daga fadar shugaban kasa kan dalilin ganawar Tinubu da Farouk Ahmed, kuma ko da ya fito, bai tsaya ya yi magana da manema labarai na.

Source: Twitter
Tashar Channel tv ta tattaro cewa lokacin da tsohon shugaban NMDPRA ya fito daga ofishin shugaban kasa, ya ce lokacin tashi aiki ya yi, don haka ba zai ce uffan ba.
"Yamma ta yi ba zai yiwu na tsaya hira da manema labarai ba. Yanzu karfe 5:00 na yamma ta wuce, don haka lokacin tashi daga aiki ya yi," in ji Farouk Ahmed.
Farouk Ahmed ya maida martani ga Dangote?
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban NMDPRA, Injiniya Farouk Ahmed, ya musanta wata sanarwa da ake cewa ya fitar kan zarge-zargen da ake yi masa.
Farouk Ahmed ya bayyana cewa yana sane da zarge-zargen da Dangote ya masa tare da iyalansa, wadanda ya bayyana a matsayin marasa tushe.
Ya ce yana da yakinin cewa binciken da ake gudanarwa zai taimaka wajen warware dukkannin shakku da kuma wanke sunansa daga duk wani zargi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


