PDP Ta Sake Birkicewa, Sanata Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC
- Sanata mai wakiltar yankin Kudancin jihar Kaduna a majalisar dattawa ya tabbatar da sauya shekarsa daga jam’iyyar adawa
- A yanzu Sunday Marshall Katung ya rabu da jam’iyyar PDP, ya shiga APC mai rinjaye a majalisar wakilai da dattawan Najeriya
- ‘Dan siyasar ya raba gari da PDP da ta ba shi damar zama Sanata, ‘dan majalisar wakilai da kuma ‘dan takara a zaben gwamna
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, Sunday Marshall Katung, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP.
Sanata Sunday Marshall Katung ya kuma sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar Tribune ta kawo rahoton cewa an karanta wasikar sauya shekar Sanata Sunday ne a gaban Majalisar Dattawa a ranar Laraba, 17 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta wasikar ga sanatoci yayin zaman majalisar.
A cikin wasikar, Sanata Marshall Katung ya ce PDP ta shiga tsaka mai wuya na rarrabuwar kai, tare da cewa jam’iyyar ba ta dace da muradun masu kada kuri’a a mazabarsa ba.
Ya kuma ce “canjin yanayin siyasa” da ke faruwa a Najeriya ya nuna a fili cewa tabbatar da makomar siyasa a gareshi da mutanen da yake wakilta na tare ne da jam’iyyar APC.
Asali: Legit.ng
