'Yan Ta'adda Sun Hargitsa Gari, Sun Kora Mutane Daji a Zamfara
- Ana zargin wasu 'yan bindiga sun bi dare inda suka kai mummunan hari a kan mazauna kauyen Zamfara suna tsaka da barci
- Harin ya faru da tsakar dare a karamar hukumar Bungudu, lamarin da ya samu jama'a babu zato ko tsammani tare da asarar rai
- Jami’an tsaro sun fara farautar masu laifin domin ceto wadanda aka sace yayin da jama'a ke ci gaba da zama cikin zulumi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara – Wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai ya sake girgiza al’ummar jihar Zamfara, yayin da dama ke zaune a cikin dardar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan ta'adda da suka kai hari garin sun kashe wani matashi tare da sace wasu mutane da dama a wani yanki na karamar hukumar Bungudu.

Source: Original
Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa harin ya jefa jama'a a cikin firgici, musamman ganin 'yan ta'addan suka bude wuta a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zamfara: 'Yan ta'adda sun kai hari a Bungudu
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta'addan sun kai harin ne a wani wuri da ake amfani da shi wajen ajiye kayayyaki, tare da kidima jama'ar da ke wurin.
Harin ya faru ne da tsakar dare, lokacin da mafi yawan mazauna yankin ke cikin barci, lamarin da ya bai wa maharan damar kai farmaki hakalinsu kwance.
Majiyoyi sun bayyana cewa harin ya auku ne da misalin 12.30 na dare a ranar 16 ga Disamba,2025 a yankin Karakkai da ke Bungudu.
‘Yan bindigan, dauke da bindigun AK-47 da sauran manyan makamai, sun rika harbe-harbe ba kakkautawa, abin da ya haddasa firgici a tsakanin jama’a.
A yayin harin, wani matashi mai suna Lukman Rabe, mai shekaru 21, ya rasa ransa bayan da harsashi ya same shi.

Kara karanta wannan
Dakarun sojojin Najeriya sun bi sawun 'yan bindiga, sun gano mutane 3 a jihar Kano
Yan ta'adda sun yi garkuwa da mutane
Baya ga haka, wasu mutane da ba a bayyana adadinsu ba sun fada hannun ‘yan bindigan, inda aka tafi da su zuwa wani wuri da har yanzu ba a sani ba.
Mazauna yankin sun bayyana cewa harin ya zo masu ba zato ba tsammani, inda suka ce irin wannan lamari na kara tsananta rayuwa da hana su gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.
Bayan aukuwar harin, jami’an sojoji tare da hadin gwiwar ‘yan sanda da kuma mafarauta sun garzaya wurin domin tabbatar da tsaro da hana yaduwar tashin hankalin.
An killace yankin tare da fara sintiri domin bin sawun maharan da zummar a cimmasu tare da ceto mutanen da suka kwashe zuwa maboyarsu.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa ana ci gaba da kokarin ceto mutanen da aka sace tare da kamo wadanda suka aikata laifin.
'Yan ta'adda sun gamu da fushin jama'a
A baya, mun wallafa cewa al’ummar kauyen Yargeda da ke Karamar Hukumar Bakura a Jihar Zamfara sun nuna fushinsu kan ta’addancin ‘yan bindiga bayan da suka kai musu hari har gida.

Kara karanta wannan
Allura ta tono garma: Tsohon hadimin Matawalle ya shirya yi masa fallasa gaban kotu
Rahotanni sun bayyana cewa jama’ar yankin sun dauki mataki kai tsaye bayan sun yi nasarar cafke mutum daya daga cikin yan ta'addan da suka kai masu hari suna zaman-zamansu lafiya.
'Yan bindiga sun kai hari kauyen Yargeda, inda suka yi garkuwa da mutane uku. Bayan farmakin, maharan sun nufi daji domin tsallakewa zuwa wani wuri da ba a sani ba, ta kusa da kauyen Rini.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
