Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Kinkimo Aiki, Zai Kashe Naira Biliyan 11 a Wata 12

Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Kinkimo Aiki, Zai Kashe Naira Biliyan 11 a Wata 12

  • Shugaban karamar hukumar Coker-Aguda, Azeez Ogidan, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2026 na sama da Naira biliyan 11
  • Kasafin kudin 2026 da Azeez ya gabatar ya mayar da hankali kan lafiya, ilimi, gine-ginen tituna, tattalin arziki da jin dadin al’umma
  • Wannan na zuwa ne yayin da wasu gwamnonin jihohi suka riga suka sanya hannu kan kasafin 2026 bayan amincewar majalisunsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Shugaban karamar hukumar Coker-Aguda (LCDA), Azeez Ogidan, ya gabatar da kudurin kasafin kudin shekarar 2026 ga majalisar karamar hukumar ta shida.

A yayin gabatar da kasafin, wanda ya haura N11bn, Azeez Ogidan ya bayyana cewa kasafin ya fito kudurin gwamnatinsa na zurfafa ci gaban kasa a matakin faro tare da tabbatar da cewa al’ummar yankin sun amfana da ayyukan gwamnati.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta shiga dambarwar Dangote da shugaban NMDPRA

Shugaban karamar hukuma a Legas zai kashe Naira biliyan 11 a wata 12
Shugaban karamar hukumar Coker-Aguda, Azeez Ogidan da 'yan majalisarsa a taron nazarin kasafin 2026. Hoto: @OgidanAzeez1
Source: Twitter

Legas: Ciyaman ya gabatar da kasafin N11bn

Shugaban karamar hukumar ya jaddada cewa kasafin kudin 2026 da ya gabatar zai fi karkata ne kan bangarori masu muhimmanci, in ji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhimman bangarorin da kasafin zai shafa sun hada da kiwon lafiya, gine-ginen tituna, ilimi, shirye-shiryen karfafa tattalin arzikin al’umma da kuma ci gaban zamantakewa.

Ya ce manufar kasafin ita ce biyan bukatu da muradun mazauna yankin Coker-Aguda, tare da tabbatar da cewa an isar da ribar dimokuradiyya ga kowa cikin gaskiya da adalci.

Ciyaman din ya kara da cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar tafiyar da mulki a bude, bisa la’akari da bukatun jama’a, da kuma gaggauta aiwatar da ayyukan ci gaba a fadin yankin.

Majalisa za ta gaggauta amincewa da kasafi

Ya ce idan aka samu karuwar kudaden shiga, hakan zai taimaka wajen tabbatar da dorewar ayyukan raya kasa da kuma cika alkawuran da aka dauka wa al’umma.

Kara karanta wannan

NMDPRA: Dangote ya garzaya ICPC, ya nemi a kama babban jami'i a gwamnatin Tinubu

Shugaban majalisar dokoki ta Coker-Aguda, Afeez Sulaiman, ya yabawa Azeez Ogidan bisa gabatar da kasafin kudin da ya mayar da hankali kan ci gaba da makomar yankin.

Ya tabbatar wa al’umma cewa bangaren majalisa a shirye yake ya tabbatar da cikakken nazari da kuma gaggauta amincewa da kudurin kasafin kudin domin fara aiwatar da shi ba tare da bata lokaci ba.

Majalisar karamar hukumar Coker-Aguda da ke Legas ta ce za ta gaggauta amincewa da kasafin 2026.
Wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin karamar hukumar Coker-Aguda lokacin bitar kasafin 2026 na N11bn. Hoto: @OgidanAzeez1
Source: Twitter

Kasafin kudi: abin da ke faruwa a wasu jihohi

Wannan na zuwa ne yayin da gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya gabatar da kasafin kudin 2026 na N939.85bn, mai taken ga majalisar dokokin jihar, in ji rahoton Punch.

Haka kuma, gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya rattaba hannu kan kasafin kudin 2026 na N642.9bn bayan majalisar dokokin jihar ta amince da shi.

A jihar Delta ma, Gwamna Sheriff Oborevwori ya sanya hannu kan kasafin kudin 2026 na N1.729tn.

Gwamna Abba ya mika kasafin N1.3tr

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da sabon kasafin kuɗi na shekarar 2026 da adadinsa ya kai N1,368,127,929,271 ga majalisar dokokin Kano.

Kara karanta wannan

An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

Kasafin kudin ya ƙunshi kashi 68 cikin 100 na kuɗin manyan ayyuka, wanda ya kai N934.6bn, yayin da kudin gudanar da gwamnati ya tsaya a N433.4bn, wato 32%.

Gwamna Abba ya fayyace cewa bangaren Ilimi ne ya samu kaso mafi tsoka da N405.3bn (30%), wanda ke nuna jajircewarsa na tallafa wa ci gaban ɗalibai da inganta makarantun jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com