An Fara Martani kan Sabon Takunkumin da Trump ya Kakabawa wa Najeriya
- Sanata Shehu Sani ya yi tsokaci mai zafi kan matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da aka kakabawa takunkumin biza
- Ya ce sakon da ke fitowa daga matakin a bayyane yake, inda aka nuna cewa ba a maraba da wasu ’yan ƙasashen duniya a manyan ƙasashe
- Kalaman Shehu Sani sun zo ne bayan gwamnatin Donald Trump ta faɗaɗa takunkumin shigar baƙi bisa dalilan tsaro da na tantancewa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sanata Shehu Sani ya yi martani kan sabon matakin da gwamnatin ƙasar Amurka ta ɗauka na kakaba takunkumin biza ga ’yan Najeriya da wasu ƙasashen Afirka da Caribbean.
Shehu Sani ya bayyana cewa sabon tsarin takunkumin ya nuna sauyi daga abin da wasu ke zato a farko, inda mutane da dama suka yi tunanin matakin zai shafi jami’an gwamnati kaɗai ne.

Source: Twitter
Martanin da ya yi a X ya biyo bayan sanarwar da shugaban Amurka, Donald J. Trump, ya fitar na faɗaɗa matakan hana shigar ’yan wasu ƙasashe cikin Amurka bisa dalilan tsaro.
Martanin Shehu Sani kan takunkumin Donald Trump
A cewar Shehu Sani, mutane na zaton takunkumin zai mayar da hankali ne kan mutanen da ake zargi da tauye ’yancin addini, lamarin da ya sa wasu suka yi murna a kafafen sada zumunta.
Sai dai ya ce matakin ya shafi kowa da kowa, musamman bayan saka Najeriya cikin jerin ƙasashe 23 da aka sanya musu takunkumin shiga Amurka.

Source: Twitter
Ya yi nuni da cewa jerin ƙasashen da aka lissafo bai haɗa da ƙasashen Larabawa ba, yayin da mafi yawansu ke daga Afirka da Caribbean, duk da cewa an jingina matakin da dalilan tsaro.
“Sakon a bayyane yake,”
“Ba a maraba da baƙin haure daga ƙasashe masu tasowa. Ku zauna ku gina ƙasarku, ko ku cigaba da fama da matsalolinku.”
Matakin Trump kan kasashen duniya
Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta faɗaɗa takunkumin shigar baƙi ga ’yan ƙasashe da dama da ake ganin suna da matsaloli a fannin tantancewa, bincike da musayar bayanan tsaro.
Shugaba Donald Trump ya sanya cikakken takunkumi kan ’yan ƙasashe 12 da tuni aka ayyana a matsayin masu haɗari, ciki har da Afghanistan, Iran, Libya, Somalia da Haiti.
Haka kuma, an ƙara wasu ƙasashe kamar Burkina Faso, Mali, Niger da Sudan ta Kudu cikin jerin waɗanda aka sanya musu cikakken takunkumi bisa sababbin rahotannin tsaro.
Dalilin saka Najeriya cikin jerin
A ɓangaren Najeriya, Zagazola Makama ya wallafa a X cewa Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashe 15 da aka kakaba musu takunkumin shiga kasar.
Gwamnatin Amurka ta jingina wannan mataki da matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya, musamman ayyukan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP a wasu yankuna.
A cewarta, irin waɗannan ƙalubale na tsaro na haifar da cikas wajen tantancewa da binciken bayanan matafiya, lamarin da ke ƙara wa hukumomin Amurka wahala.
Amurka ta gargadi 'yan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta gargadi 'yan Najeriya masu neman biza da su guji amfani da bayanan bogi.
Ofishin jakadancin Amurka da ke birnin tarayya Abuja ne ya bayyana haka, inda ya ce yana bincike mai zurfi kan bayanan jama'a.
Legit ta wallafa cewa gwamnatin Amurka ta yi gargadi da cewa za a hana duk wanda aka kama da takardun bogi shiga kasar har abada.
Asali: Legit.ng


