Bayan Suka Ta Ko Ina, An Dakatar da Yi wa Dogarin Tinubu Karin Girma

Bayan Suka Ta Ko Ina, An Dakatar da Yi wa Dogarin Tinubu Karin Girma

  • An janye maganar yi wa Kanal Nurudeen Yusuf karin matsayi a gidan soja a matsayinsa na Dogarin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
  • Tsofaffin hafsoshin sojin kasa biyu sun shiga tsakani, lamarin da ya sa aka dakatar da nadin ana dab da kara masa girma zuwa Birgediya Janar
  • Masana harkar soji sun gargadi cewa irin wannan karin girma na musamman na iya zama mummunan abin koyi ga rundunar a nan gaba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shirin daukaka dogarin Shugaban Kasa (ADC), zuwa mukamin Brigediya Janar da ya tayar da kura ya gamu da matsala.

Rahotanni sun bayyana cewa a daren Litinin, wasu hafsoshin sojin kasa biyu suka tsoma baki a lamarin da nufin kawo daidaita a tsarin soja.

Kara karanta wannan

An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

An dakatar da kara wa mai tsaron Tinubu girma
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

A labarin da ya kebanta ga Jaridar The Cable, an ji yanzu an dakatar da shirin kara wa Nurudeen Yusuf girma saboda fargabar illar da hakan ka iya yi wa tsarin rundunar sojin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dakatar da karawa hadimin Tinubu girma

Daily Post ta wallafa cewa Nurudeen Yusuf, ya samu karin girma zuwa mukamin Kanal a watan Janairun da ya gabata, wanda ya sa aka yi tirjiya a shirin sake kara masa matsayi.

A tsarin soji na yau da kullum, dole ne jami’i ya shafe akalla shekaru hudu a matsayin Kanal, sannan ya halarci Kwalejin Tsaro ta Kasa (NDC) kafin a yi la’akari da daukaka shi.

Ana zargin Nuhu Ribadu ya sa hannu a kan takardar neman a kara wa Nurudeen Yusuf girma
Mashawarcin Bola Tinubu game da tsaro, Nuhu Ribadu Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Facebook

A cewar rahotanni, an aike wasika da ke neman kaucewa wannan tsari daga ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) zuwa ga babban hafsan sojin kasa.

Wasikar, wacce aka ce ta fita a ranar 12 ga Disamba, 2025, kuma Nuhu Ribadu, ya sanya hannu a kanta, ta nuna cewa Yusuf zai ci gaba da zama dogari ga shugaban kasa ko bayan samun mukamin Birgediya Janar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sa labule da hafsoshin tsaro bayan amincewa da tura sojoji Benin

An fusata da shirin kara wa ADC girma

Sai dai wannan mataki ya kara tada hankula ganin cewa babu wani Janar mai tauraro daya da ya taba zama mai tsaron Shugaban kasa a tarihin Najeriya.

Kafin ranar da aka tsara kawata Nurudeen Yusuf din, Ministan tsaro, Janar Chris Musa mai ritaya, da Hafsan hafsoshin tsaro na kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, sun katse ziyararsu a Legas suka dawo Abuja.

Daga bisani, tsofaffin hafsoshin soji biyu sun shawo kan Shugaba Tinubu da ya dakatar da shirin gaba daya bayan zazzafan muhawara da kokarin karin girman ya jawo.

An gano illar karin girman ga tsarin soja

Wata majiya daga fadar Shugaban kasa ta shaida cewa an jingine batun kara wa dogarin Shugaban Kasa girma zuwa gaba.

Masana harkar soji da dama sun bayyana cewa matakin zai zama mummunan abin koyi, tare da barazana ga daidaito da martabar rundunar.

A baya, an zargi Nurudeen Yusuf da amfani da kusancinsa da Shugaban Kasa wajen yin tasiri a kan daukaka da ci gaba da rike mukamai ga wasu jami’an soji.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya tsage gaskiya kan matsalar rashin tsaro a Najeriya

Wata majiya ta soji ta ce an taba sanya Shugaban Kasa ya rattaba hannu kan takardar daukaka jami’an da suka kusa ritaya bayan sun fadi jarabawa sau uku.

Bola Tinubu ya yi wa talakawa albishir

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake kwantar da hankalin ’yan Najeriya kan sabbin dokokin haraji da gwamnatinsa ta ƙirƙiro, inda ya tabbatar da cewa za a amfana.

Tinubu ya kara da cewa manufofin za su kasance masu amfani ga talakawa, masu ƙaramin albashi da kuma ’yan kasuwa masu matsakaicin ƙarfi duk da fargabar da ake a kan batun harajin.

Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne yayin da ake ci gaba da muhawara da fargaba a wasu sassa na ƙasar game da tasirin sababbin dokokin haraji da za su fara aiki a sabuwar shekara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng