Manyan Arewa Sun Ziyarci CAN da JNI domin Hada kan Musulmi da Kirista
- Wasu fitattun shugabannin Arewa sun fara yunkurin sulhu ta hanyar ziyartar CAN da JNI domin rage rashin fahimta tsakanin Musulmi da Kiristoci
- Kungiyar da aka kafa kwanan nan ta ce lokaci ya yi da Arewa za ta fuskanci matsalolin da rikice-rikice suka haifar ta hanyar sulhu da hadin kai
- A lokacin ziyarar, shugabannin addinai sun nuna goyon baya, suna bayyana cewa sabuwar muryar neman zaman lafiya na kara karfi a yankin Arewa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Wasu manyan shugabanni daga Arewa, ciki har da tsohon kakakin NEF, Dr Hakeem Baba Ahmed, sun kai ziyara hedikwatar Kungiyar Kiristocin Najeriya ta jihohi 19 na Arewa da kuma Jama’atu Nasril Islam.
Ziyarar ta kasance karkashin wata sabuwar kungiya da aka kafa mai suna Northern Reconciliation Group, wacce ta kunshi ‘yan Arewa Musulmi da Kiristoci da ke da manufa daya ta karfafa zaman lafiya da hadin kai.

Kara karanta wannan
An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa manufar ziyarar, a cewar jagororin tawagar, ita ce bude sabon babi na tattaunawa da fahimtar juna, domin kawo karshen rikice-rikicen da suka dade suna addabar Arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin kafa sabuwar kungiyar 'yan Arewa
Dr Hakeem Baba Ahmed, wanda ya jagoranci tawagar, ya ce an kafa kungiyar Northern Reconciliation Group ne bisa fahimtar cewa Arewa ta sha wahala matuka sakamakon rikice-rikice da rashin jituwa.
Ya bayyana cewa ‘yan kungiyar sun hadu ne a matsayin ‘yan Arewa, ba tare da la’akari da bambancin addini ba, domin su daura yankin a turbar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A cewarsa, Musulmi da Kiristoci duk halittar Allah ne, kuma duk da bambancin akidu, an halicce su a matsayin al’umma daya da ya kamata su zauna lafiya da juna.
Batun hada kan Musulmi da Kiristocin Arewa
Dr Hakeem ya jaddada cewa lokaci ya yi da Musulmi da Kiristoci a Arewa za su tsaya tsayin daka su zabi zaman lafiya maimakon rikici.
Vanguard ta rahoto cewa ya ce kungiyar ta fahimci cewa babu wata al’umma da za ta ci gaba idan tana fama da rabuwar kai, musamman ganin yadda rikice-rikice suka yi wa Arewa illa ta fuskar rayuka, dukiyoyi da ci gaban zamantakewa.

Source: UGC
Ya kara da cewa manufar wannan yunkuri ita ce karfafa fahimtar juna da gina amana tsakanin mabiyan addinai biyu.
Martanin CAN kan yunkurin sulhu
Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya ta jihohi 19 na Arewa, Joseph John Hayab, ya bayyana cewa ziyara irin wannan na da matukar muhimmanci ga makomar yankin.
Ya ce duk da cewa an sha fuskantar fada da rashin fahimta a Arewa, yanzu akwai wata sabuwar murya da ke cewa ya isa haka, kuma dole ne a nemo mafita.
Bayanin JNI kan hada kan 'yan Arewa
A nasa bangaren, Sakataren Janar na Jama’atu Nasril Islam, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya ce duk lokacin da mutane suka hada kai domin warware matsala, taimakon Allah kan zo.
Ya bayyana cewa JNI na maraba da wannan yunkuri, yana mai jaddada cewa hadin kai tsakanin Musulmi da Kiristoci ne ginshikin zaman lafiya mai dorewa.
A shekarar 1962 aka kafa Jama’atu Nasril Islam ta sanadiyyar Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto.

Kara karanta wannan
Matawalle: Kungiya ta ba Tinubu shawarar abin da ya dace da karamin Ministan tsaro
An kashe musulimi 4,700 a Filato
A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto muku cewa wata kungiya a Filato ta bayyana adadin Musulmai da aka kashe a jihar.
A wani taron addu'a da aka gudanar domin tunawa da wadanda suka rasu, kungiyar ta ce akalla Musulmai 4,700 aka kashe.
Shugaban kungiyar ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta ta jihar Filato da su cigaba da daukar matakan kare rayukan jama'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
