Majalisar Wakilai Ta Shiga Dambarwar Dangote da Shugaban NMDPRA

Majalisar Wakilai Ta Shiga Dambarwar Dangote da Shugaban NMDPRA

  • Majalisar Wakilai ta yanke shawarar binciken rikicin da ya barke tsakanin attajirin 'dan kasuwa, Aliko Dangote da shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed
  • Matakin ya biyo bayan kudurin gaggawa da wani dan majalisa daga Jihar Borno ya gabatar, yana mai gargadin barazanar rikicin ga samar ga farashin man fetur
  • Majalisar ta umurci kwamitoci su shiga tsakani tare da gabatar da mafita cikin makonni hudu domin shawo kan matsalar a cikin gaggawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da kudurin da zai ba wa kwamitocinta damar binciken rikicin da ke tsakanin manyan jami'ai a bangaren man fetur a Najeriya.

Za ta shiga tsakanin rikicin Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, da Farouk Ahmed,Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur NMDPRA.

Kara karanta wannan

Jita jitar mutuwar Akpabio ta harzuka majalisa, ta dauki mataki

Majalisa za ta shiga tsakanin Dangote da Farouk Ahmed
Shugaban NMDPR Farouk Ahmed, Shugaban rukunonin kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote Hoto: Hoto: @NMDPRA_Official, Dangote Industries
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa an cimma wannan matsaya ne bayan amincewa da kudurin da aka bayyana a matsayin na gaggawa kuma mai muhimmanci ga jama’a a zaman majalisar ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa za ta shiga tsakanin Dangote da Farouk

Midala Balami, 'dan majalisa mai wakiltar mazabar Askira Uba/Hawul ta Jihar Borno ne ya gabatar da kudirin gaggawar domin neman a shiga tsakani.

A yayin gabatar da kudurin, Balami ya bayyana cewa rikicin da bai warware ba tsakanin Dangote da Ahmed na iya zama barazana ga daidaiton samar da man fetur da kuma farashinsa a kasar nan.

A baya-bayan nan, Aliko Dangote ya zargi Farouk Ahmed da kashe kusan Dala miliyan biyar wajen biyan kudin karatun sakandare na ’ya’yansa hudu a kasar Switzerland tsawon shekaru shida.

Kwamitin majalisa zai ba da rahoto game da rikicin Dangote da Farouk
Wasu daga cikin 'yan Majalisar Wakilan Najeriya Hoto: House of Representatives
Source: Facebook

Dangote ya ce kudin karatu, jirgin sama da kula da kowane yaro ya kai $200,000 a shekara, wanda ya zama $800,000 a shekara ga yara hudu.

Kara karanta wannan

An samu 'yar hatsaniya a zaman tantance jakadu a Majalisar Dattawa

Ya kara da cewa jimillar kudin kula da su da tikitin jirgi na tsawon shekaru shida sun kai $1.2m, lamarin da ya kai adadin kusan $4.8m gaba daya.

Yadda rikicin Dangote da NMDPRA ya yi kamari

Rikicin Dangote da Ahmed ya kara tsananta ne a watan Yulin 2024, lokacin da shugaban NMDPRA ya bayyana cewa matatun mai na cikin gida, ciki har da matatar Dangote, na samar da man fetur marar inganci.

Dangote ya musanta wannan ikirari inda ya gudanar da gwajin dizal daga matatarsa a gaban ’yan majalisar tarayya da suka kai ziyarar duba aiki a matatar.

'Dan majalisa Balami ya jaddada cewa Dangote na taka muhimmiyar rawa wajen rage dogaro da shigo da man fetur daga waje, adana kudaden waje, daidaita wadatar mai a cikin gida, da rage tashin farashin man fetur.

Saboda haka, ya ce rikicin da ke tsakaninsa da shugaban NMDPRA na bukatar daukar mataki cikin gaggawa domin dakile duk wani abu da zai jawo matsalar farashin man fetur.

Majalisar ta amince da kudurin baki daya bayan mataimakin kakakin majalisa, Benjamin Kalu, ya gabatar da shi ga kuri’ar murya.

Kara karanta wannan

Gwamna zai zuba jarin Naira biliyan 3.5 domin inganta makarantun musulmai a jiharsa

Daga nan ne aka umurci kwamitocin majalisar kan albarkatun man fetur su binciki rikicin, su tuntubi masu ruwa da tsaki, tare da gabatar da shawarwari cikin makonni hudu.

NMDPRA: Dangote ya garzaya ICPC

A baya, mun wallafa cewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng