Mangal Ya Samu Mukami da Gwamna Radda Ya Kaddamar da Majalisar Sarakunan Katsina

Mangal Ya Samu Mukami da Gwamna Radda Ya Kaddamar da Majalisar Sarakunan Katsina

  • Gwamna Dikko Umaru Radda ya kaddamar da majalisar masarautun jihar Katsina don karfafa dangantakar gwamnati da sarakuna
  • Sarkin Katsina ya zama shugaban majalisar, yayin da sarkin Daura ke matsayin mataimaki, tare da wakilan addini, 'yan kasuwa da matasa
  • Majalisar za ta ba da shawarwari kan shari’a, al’adu, tsaro, zaman lafiya, raya al’umma da kare muhalli a Katsina, a cewar Dikko Radda

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, kafa tarihi yayin da ya kaddamar da majalisar masarautun Katsina.

Gwamna Dikko Radda ya ce kafa majalisar ne domin zurfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da manyan sarakunan gargajiya.

Gwamna Dikko Radda ya kaddamar da majalisar sarakunan Katsina
Gwamna Dikko Radda, Sarkin Katsina da na Daura, 'yan kasuwa, da manya a taron kaddamar da majalisar sarakunan Katsina. Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

An kaddamar da Majalisar sarakunan Katsina

Mai magana da yawun gwamna, Ibrahima Kaulaha Mohammed, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta shiga dambarwar Dangote da shugaban NMDPRA

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta rahoto Gwamna Radda ya ce kaddamar da majalisar zai taimaka wajen inganta tafiyar da mulki, da kuma tabbatar da zaman lafiya da hadin kan al’umma a fadin jihar.

A jawabin da ya gabatar yayin kaddamar da majalisar a gidan gwamnatin Katsina, Gwamna Radda ya ce:

“Wannan babbar rana ce mai matukar muhimmanci da tarihi. Yau rana ce da za a rika tunawa da ita a tarihin jihar Katsina, domin mun kaddamar da majalisar masarautun Katsina domin karfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masarautun gargajiya da muke girmamawa.”

Tsarin shugabancin majalisar sarakunan Katsina

Gwamna Radda ya sanar da cewa sarkin Katsina ne shugaban majalisar masarautun Katsina, yayin da sarkin Daura zai rike da mukamin mataimakin shugaba.

Ya bayyana cewa mambobin majalisar sun hada da manyan masu nada sarki daga masarautar Katsina, wadanda suka hada da Kauran Katsina, Yandakan Katsina, Galadiman Katsina, Durbin Katsina da Marusan Katsina.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fadawa Tinubu abin da zai yi don hana manoman Najeriya tafka asara

Daga bangaren masarautar Daura kuma, mambobin sun hada da Galadiman Daura, Kauran Daura, Limamin Juma’a, Dansawai da Fada Babba na Daura.

Gwamnan ya kara da cewa sakataren gwamnatin jihar Katsina na daga cikin mambobin majalisar, tare da Ambasada Ahmed Rufai, Sardaunan Katsina; Ambasada Adamu Saeed Daura; da Alhaji Hamza Abu Duwan, Madawakin Katsina.

Haka kuma, majalisar ta kunshi wakilai daga bangarorin 'yan kasuwa, addini da matasa. Wadannan sun hada da Alhaji Dahiru Barau Mangal da Alhaji Baba Buhari, Walin Daura; Sheikh Yakubu Musa Hassan da Sheikh Naziru Kofar Baru na Daura; da Abdulaziz Abdulaziz Malumfashi.

Sanata Ibrahim Mohammed Ida, Wazirin Katsina, shi ne sakataren majalisar, yayin da Sada Salisu Danwairen Katsina zai rike da mukamin mataimakin sakatare.

Ayyuka da rawar da majalisar za ta taka

A cewar Gwamna Radda, majalisar masarautun Katsina za ta rika ba gwamnan shawara kan harkokin shari’ar Musulunci da ta gargajiya, al’adu, harkokin sarauta da lamuran al’umma.

Har ila yau, majalisar sarakunan za ta ba da shawarwari kan tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kiyaye doka da oda idan bukatar hakan ta taso.

Kara karanta wannan

Bayan rantsar da kwamishinoni, Gwamna Umaru Bago ya fatattaki hadimai sama da 25

Gwamnan ya bayyana cewa majalisar za ta kuma taimaka wa gwamnati wajen raya al’umma, tallafawa hukumomin karbar haraji, inganta kare muhalli da gandun daji, sa ido kan tsaftar muhalli, da kuma kare kyawawan al’adu da dabi’un gargajiya na jihar Katsina.

Gwamna Radda ya ce majalisar sarakuna za ta rika taimakawa gwamna a wajen ba da shawarwari
Sarkin Katsina ya zama shugaban majalisar sarakunan Katsina, yayin da Sarkin Daura ya zama mataimaki. Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Gwamna ya yi addu’a ga mambobin majalisar

Gwamna Radda ya taya dukkan mambobin majalisar murna bisa zabarsu da aka yi, inda ya yi musu fatan sauke nauyin da aka dora musu domin samun ci gaba, zaman lafiya da hadin kai a jihar Katsina.

Ya ce:

“A madadin gwamnatin jihar Katsina, ina taya dukkan mambobin da aka zaba murna. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki Ya rike hannayenku wajen gudanar da ayyukanku domin ci gaban zaman lafiya da daidaito a jiharmu.”

Manyan jami’an da suka halarci taron

Manyan jami’an gwamnati da suka halarci bikin kaddamarwar sun hada da sakataren gwamnatin jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari da alkalin alkalan jihar Katsina Mai shari’a Musa Abubakar Danladi.

Sauran sun hada da shugaban ma’aikatan gidan gwamna, Abdulkadir Mamman Nasir; babban sakataren gwamna na musamman, Abdullahi Aliyu Turaji; da mambobin majalisar zartarwa ta jihar Katsina.

Sarkin Ruman Katsina ya rasu

A wani labari, mun ruwaito cewa, Sarkin Ruman Katsina, Alhaji Tukur Mu'azu ya rasu yana da shekaru 76 da haihuwa a ranar Litinin, 22 ga Satumba, 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya kafa tarihi a bangaren samar da wutar lantarki ga talakawa

Rahotanni sun nuna cewa marigayin, wanda shi ne hakimin Batsari, ya dade yana fama da rashin lafiya kafin ya koma ga Allah a gidansa da ke Batsari, jihar Katsina.

Sanarwar da iyalan mamacin suka fitar ta nuna cewa an yi jana'izar basaraken bayan sallar La'asar, da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar, bisa koyarwar addini.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com