Bayan Zama da DSS, Abba Ya Yi Nasarar Hana Ganduje Kafa Hisbah a Kano
- Abdullahi Umar Ganduje ya janye shirin kafa Hisbah mai zaman kanta bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da hukumomin tsaro a jihar Kano
- An dauki matakin ne bayan ganawar da ta hada wakilai daga kananan hukumomi 44, jiga-jigan APC na Kano da jami’an DSS, inda aka tattauna zaman lafiya
- Sai dai wasu kalamai daga na kusa da Ganduje sun nuna cewa ana ci gaba da duba shirin, lamarin da ke kara tayar da rade-radi kan makomar batun
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya dakatar da shirin kafa Hisbah mai zaman kanta a jihar, bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma hukumomin tsaro.
Matakin ya biyo bayan koke-koken jama’a da kuma shawarwarin da aka bayar domin kauce wa tashin hankali da rikici, musamman ganin irin rawar da Hisbah ke takawa a Kano.

Source: Facebook
Tashar Arise News ta rahoto cewa sanarwa da aka fitar bayan ganawar masu ruwa da tsaki ta bayyana cewa an dauki wannan matsaya ne domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano da kasa baki daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin dakatar da Hisbar Ganduje a Kano
A cewar sanarwar da Alhaji Baffa Babba Dan Agundi ya sanya wa hannu a madadin Ganduje, an dakatar da shirin kafa Hisbah mai zaman kanta ne bayan yin la’akari da ra’ayoyin jama’a da kuma tsoma bakin hukumomin tsaro.
Sanarwar ta ce kokarin kafa Hisbah mai zaman kanta ya fuskanci suka daga sassa daban-daban na al’umma, inda aka nuna damuwa kan yiwuwar samun rikici ko rikitarwa a harkokin tsaro da gudanar da doka.
Haka kuma, gwamnatin jihar Kano da hukumomin tsaro sun shiga tsakani domin tabbatar da cewa duk wani mataki da za a dauka bai haifar da tashin hankali ba, lamarin da ya sa aka dakatar da shirin gaba daya.
Abin da taron masu ruwa da tsaki ya cimma
Taron tuntuba da aka gudanar a Kano ya hada wakilai daga kananan hukumomi 44 na jihar, jiga-jigan jam’iyyar APC da kuma jami’an DSS.
A taron, an yanke shawarar dakatar da shirin kafa Independent Hisbah Fisabilillah, tare da bai wa gwamnatin jihar Kano damar warware zarge-zargen da ake yi wa hukumar Hisbah ta jihar a halin yanzu.

Source: Twitter
Mahalarta taron sun jaddada muhimmancin mutunta doka da oda, tare da bukatar yin aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro a fadin jihar.
Sabani kan ko shirin ya kare gaba daya
Duk da sanarwar dakatar da shirin, hadimin Ganduje, Mohammed Garba, ya bayyana cewa shirin kafa Hisbah mai zaman kanta na ci gaba da fuskantar gyare-gyare.
Garba ya cewa The Cable ana yin wadannan sauye-sauye ne domin tabbatar da cewa shirin bai yi karo da Hisbah ta jihar Kano ba, yana mai cewa ana la’akari da damuwar da wasu mutane da kungiyoyi suka nuna.
Abba ya haramta Hisbar Ganduje a Kano
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya haramta Hisbar da Abdullahi Umar Ganduje zai kafa.
Alhaji Abba Kabir ya bukaci jami'an tsaro su gaggauta cafke masu daukar matasa aikin bayan fara raba fom a fadin jihar Kano.
A sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, ta bukaci dukkan wadanda aka dauka aikin Hisbar Ganduje su mika kansu ga hukuma.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


