Majalisa Ta Fadawa Tinubu abin da Zai Yi don Hana Manoman Najeriya Tafka Asara

Majalisa Ta Fadawa Tinubu abin da Zai Yi don Hana Manoman Najeriya Tafka Asara

  • Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta rage farashin taki domin kare rayuwar manoma da dorewar samar da abinci
  • Sanatoci sun ce raguwar farashin amfanin gona tare da tsadar kayan noma na haddasa asara, talauci, da barazana ga tsaron abinci
  • Majalisar ta bukaci a samar da tallafi mai fadi kan taki, magungunan, da kammala rumbuna domin tallafa wa manoma a fadin kasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin Bola Tinubu da ta dauki matakin gaggawa domin rage farashin taki da sauran kayan noma.

A cewar majalisar dattawan, rage kudin taki ne zai kare rayuwar manoman Najeriya da kuma tabbatar da dorewar samar da abinci a kasar.

Majalisa ta bukaci Tinubu ya rage kudin taki da kayan noma don ceto manoman Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya samu kira daga majalisa kan halin da manoman Najeriya ke ciki. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Facebook

An fadawa Tinubu halin da manoma ke ciki

Wannan matsaya ta biyo bayan wani kudiri da Sanata Danjuma Goje, mai wakiltar Gombe ta Tsakiya, ya gabatar a zaman majalisar ranar Talata, in ji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Bayan zama da DSS, Abba ya yi nasarar hana Ganduje kafa Hisbah a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Goje ya yabawa gwamnatin Tinubu kan matakan da ta dauka na rage farashin abinci ta hanyar bada tallafi da kuma amincewa da shigo da kayan masarufi da yawa daga kasashen waje.

Sai dai ya ce, duk da saukin farashin abinci da jama’a ke samu, hakan ya janyo mummunar illa ga manoman cikin gida.

“Yayin da farashin amfanin gona ke ci gaba da raguwa, farashin kayan noma kamar taki, magungunan kwari da sauran su na ci gaba da tsada matuka,” in ji Goje.

Tsohon gwamnan Gombe ya bayyana cewa wannan yanayi ya janyo asarar amfanin gona bayan girbi, inda manoma ke kasa sayar da kayan su, lamarin da ke haddasa lalacewa da asarar kudaden shiga.

Sanatoci sun nemi sassauci ga manoma

Ya gargadi cewa idan ba a dauki mataki ba, hakan na iya rage yawan noma a kasar, ya durkusar da tattalin arzikin karkara, tare da kara raunana tsaron abinci na kasa.

Kara karanta wannan

Jirgin ruwan Najeriya da wasu kasashe da suka fada tarkon Amurka a 2025

Sanata Aliyu Wamakko na Sokoto ta Arewa ya mara wa kudirin baya, yana mai cewa tsadar taki da sauran kayan noma abin damuwa ne sosai.

Sanata Mohammed Dandutse na Katsina ta Kudu ya ce sama da kashi 60 cikin 100 na ‘yan Najeriya na dogaro da noma domin rayuwa, in ji rahoton jaridar Punch.

Shi ma Sunday Karimi daga Kogi ta Yamma ya bukaci a samar da daidaito tsakanin saukin farashin abinci da kare walwalar manoma da ke kasar.

Majalisa ta ce faduwar farashin amfanin gona da tsadar kayan noma ya jawo manoma na asara a Najeriya.
Manoma mata na aiki tukuru a cikin wata gonar kayan miya. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Bukatar majalisar dattawa ga Tinubu

Wasu sanatoci sun bukaci a sanya idanu kan farashin kayayyaki, yayin da wasu suka jaddada rawar da jihohi za su taka wajen tallafawa shirye-shiryen noma na tarayya.

Sanata Patrick Ndubueze na Imo ta Arewa ya bukaci gwamnati ta kammala manyan rumbunan ajiya da aka bari a kasar, tare da amfani da su wajen sayen amfanin gona daga hannun manoma.

Bayan muhawara, majalisar dattawa ta aika bukata ga gwamnatin tarayya ta kaddamar da tallafi mai fadi kan taki da sauran kayan noma, domin kare manoma, bunkasa samar da abinci, da kuma tabbatar da tsaron abinci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamna Abba ya dauki sabon mataki don kare rayuka a Kano

Gwamnati na fatan karya farashin taki

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta ce kwamitin kula da tattalin arzikin kasa (EMT) zai dauki mataki mai tsauri kan matsalar fasa-kwaurin kayayyakin gona.

Wannan matakin, a cewar gwamnati, zai taimaka wajen daidaita farashin kayayyakin abinci da kuma kara tabbaci ga masu zuba jari a sashen sarrafa kayayyakin noma.

A cewar gwamnati, idan aka aiwatar da matakin, hakan zai sa manoman cikin gida sun ci gaba da zama masu karfi wajen gogayya da kayayyakin da ake shigowa da su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com