Bayan Rantsar da Kwamishinoni, Gwamna Umaru Bago Ya Fatattaki Hadimai Sama da 25
- Gwamnan Niger, Mohammed Umaru Bago, ya kori hadimai 30 a wani mataki na sake fasalin tsarin gwamnati da inganta ayyukan mulki
- Matakin ya biyo bayan rantsar da sababbin kwamishinoni da shugabannin kananan hukumomi, da na hukumomin gwamnatin jihar
- Gwamna Bago ya jaddada cewa ajandar 'Sabuwar Neja' na bukatar jajircewa, ladabi da aiki da basira domin kawo ci gaba ga al’umma
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umaru Bago, ya sanar da dakatar da masu ba shi shawara na musamman har su 30 da ke aiki a karkashin gwamnatinsa.
Korar mashawarta na musamman, na daga cikin matakan Umaru Bago na sake fasalin tsarin mulki da gudanarwa a jihar Bago, a cewar rahotanni.

Source: Facebook
Gwamna Bago ya kori masu bashi shawara 30
Babban sakataren yada labarai ga gwamnan, Bologi Ibrahim, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, in ji rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bologi Ibrahim ya ce Gwamna Bago ya sanar da korar ne a yayin taron majalisar zartarwa na farko da ya gudanar da sababbin kwamishinonin da aka rantsar.
A cewar sanarwar, an kori wadannan mashawarta ne domin bai wa gwamnan damar sake tsara mukamansu da ayyukansu, ta yadda za su dace da sabuwar manufar gwamnatin jihar, wato ajandar 'Sabuwar Neja'.
Ya ce gwamnan ya yaba da gudunmawar da mashawartan suka bayar a lokacin da suke aiki, tare da yi musu fatan alheri a duk inda rayuwa za ta kai su nan gaba.
Gwamna Bago ya rantsar da kwamishinoni
Wannan mataki ya zo ne kwanaki kadan bayan da Gwamna Umaru Bago ya rantsar da kwamishinoni 30, shugabannin kananan hukumomi 25 da mataimakansu, da kuma mambobin kwamitocin hukumomin jihar daban-daban.
An gudanar da bikin rantsarwar ne a dakin taro na Hauwa Wali da ke fadar gwamnatin jihar a Minna, inda babbar alkalin jihar, Halima Abdulmalik, ta jagoranci rantsar da jami’an.
A jawabinsa, Gwamna Bago ya ce an zabi dukkan sababbin jami’an ne bisa kwarewa da tarihin ayyukansu, yana mai bayyana kwarin gwiwarsa cewa za su bayar da gudunmawa mai ma’ana wajen ci gaban jihar.
Ya bukace su da su kalli kura-kuran da aka taba fuskanta a baya, su kuma hada kai wajen gina jihar Niger mai dorewa, wadda ta kunshi kowa da kowa.

Source: Twitter
Gargadi daga sakataren gwamnatin Neja
A nasa bangaren, sakataren gwamnatin Neja, Abubakar Usman, ya tunatar da sababbin kwamishinoni nauyin da ke rataye a wuyansu, yana mai cewa rawar da za su taka ce za ta tabbatar da nasarar gwamnatin.
Ya kara da cewa an shirya musu taron bita domin daidaita fahimtarsu da manyan abubuwan da gwamnati ta sanya a gaba, tare da fayyace musu abin da ake sa ran za su cimma a mukamansu.
Wasu daga cikin jami’an da aka rantsar sun nuna godiya ga gwamnan bisa damar da ya ba su, inda suka sha alwashin yin aiki tukuru domin tabbatar da nasarar ajandar 'Sabuwar Neja.'
Bago ya gano masu tallafawa 'yan bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Umaru Bago, ya ce masu bada bayanai (infomomi) na taka muhimmiyar rawa wajen ayyukan 'yan ta'adda.
Gwamna Bago ya bayyana cewa zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’ummomi na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro a jihar Neja.
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ’yan bindiga suka mamaye gandun dajin Borgu, inda ya roki gwamnati ta tarayya da ta jiha su tserar da yankin daga hannun miyagu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


