‘Buhari Ya Zargi Ana Bibiyarsa’: ’Yarsa Ta Fadi Yadda Suke Magana a Boye

‘Buhari Ya Zargi Ana Bibiyarsa’: ’Yarsa Ta Fadi Yadda Suke Magana a Boye

  • ’Yar marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ta ce mahaifinta ya taɓa zargin ana sa masa na’urorin sauraro a ofishinsa
  • Fatima Buhari ta bayyana cewa zargin ya sa su rika sadarwa ta rubuce, maimakon magana, saboda tsoron leƙen asiri
  • An ce Buhari ya yi shiru kan lamarin saboda imaninsa da halayyarsa, duk da fargabar barazana ga rayuwarsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Yar marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta yi magana game da lokacin da suke fadar Aso Rock.

Fatima Buhari ta mahaifinta ya taɓa zargin cewa an dasa masa na’urorin sauraron asiri a ofishinsa da ke Fadar Shugaban Ƙasa.

Yar Buhari ya magantu lokacin mulkin mahaifinta
Tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Facebook

Yar Buhari ta fadi faman da suka sha

Wannan bayani na kunshe ne a cikin wani sabon littafi da Dr. Charles Omole, ya rubuta kuma aka ƙaddamar da shi a Abuja, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Jita jita ta kare, Aisha Buhari ta bayyana cutar da ta yi ajalin Shugaba Buhari a Landan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Fatima, wannan zargi ya sa ita da mahaifinta suka daina magana kai tsaye a wasu lokuta, suka koma rubuta saƙonni domin sadarwa.

Ta ce a wasu lokuta marigayi Buhari kan ji tsoron cewa ana sauraron duk abin da ake faɗa a ofishinsa, lamarin da ya sa suke ɗaukar matakan kariya na musamman yayin ganawa.

Ta tuna wani lokaci da mahaifinta bai yi magana ko kaɗan ba, sai dai ya yi amfani da alamu da motsin jiki don nuna mata cewa kada su yi magana, su rubuta kawai.

“Ya kan taɓa kumatunsa kamar yana jin ciwon haƙori, yana nuna min cewa kada mu yi magana.
“Muna rubuta saƙonni ga juna kamar ’yan leƙen asiri a fim."
Fatima Buhari ta fadi yadda mahaifinta ya yi mulki cikin fargaba
Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari. Hoto: Bashir Ahmad.
Source: Twitter

Zargin da Buhari a fadarsa

Fatima ta ce Buhari ya yi imanin cewa an dasa na’urorin sauraro a ofishinsa da ke Villa, inda ya gargade ta da ta kasance mai taka-tsantsan.

Kara karanta wannan

Tonon silili: Aisha Buhari ta fadi kuskuren da mijinta ya yi a lokacin mulkinsa

Abin da ya fi tayar da hankali, a cewar littafin, shi ne yadda Buhari ya amince da wannan yanayi duk da kasancewarsa Babban Kwamandan Rundunonin Sojin Najeriya.

Fatima ta tambayi irin ƙarfin ikon mutanen da ake kira “cabal”, wadanda ake zargin suna da hannu wajen dasa na’urorin, musamman ganin cewa abin ya faru ne a cikin Villa mai tsananin tsaro.

Littafin ya kuma nuna cewa wasu manyan jami’an tsaro da suka yi aiki da Buhari daga baya sun tabbatar da cewa ana yawan gano wasu abubuwa a ofishinsa da ɗakinsa yayin binciken tsaro, duk da cewa ba a san yadda suka shiga wuraren ba.

A cewar littafin, halayen Buhari na mutunci da imani sun yi tasiri kan yadda yake magance irin waɗannan matsaloli, cewar Vanguard.

Ta ƙara da cewa da zarar Buhari ya yarda da mutum, yana da wuya ya janye amincewarsa sai idan hujja ta yi yawa, inda ya fi son gyara a ɓoye fiye da korar mutum ko kunyata shi.

'Dalilin Buhari na kin korar wasu ministoci' - Aisha

A wani labarin, Aisha Buhari ta bayyana dalilan da suka sa marigayi tsohon shugaban kasa bai sallami ministoci da hadimansa da suka gaza a aiki ba.

Kara karanta wannan

Bayan gama idda, Aisha Buhari ta yi matsaya kan sake aure

Uwargidan tsohon shugaban kasar ta ce tsufa da tsoron a kira shi 'mai kama-karya' sun sa Buhari ya yi taka-tsantsan a mulkinsa.

Sai dai, bayan sauka daga mulki, EFCC ta gurfanar da wasu jami’an gwamnatin Buhari kan zarge-zargen almundahanar biliyoyin Naira.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.