Jita Jitar Mutuwar Akpabio Ta Harzuka Majalisa, Ta Dauki Mataki
- Wasu rahotanni sun karade shafukam sada zumunta masu cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi bankwana da duniya
- Lamarin ya jawo Sanata Titus Zam ya yi magana a majalisar dattawa kan bukatar a zakulo masu yada labaran na karya
- Majalisar Tarayyar ta cimma matsayar bukatar ofishin NSA da hukumar DSS su binciko masu yada wadannnan karairayin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta yi martani kan rahotannin da ke cewa shugabanta, Sanata Godswill Akpabio ya mutu.
Majalisar ta bukaci Ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) da hukumar DSS, su bincika tare da gano mutanen da ke da hannu a rahotannin da ke cewa Akpabio ya rasu a Landan.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta ce Sanata Titus Zam, mai wakiltar mazabar Benue ta Arewa maso Yamma, ne ya tayar da batun a zaman majalisar ranar Talata, 16 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan
Akpabio ya yanke jiki fadi a ofis sakamakon rashin lafiya? An ji gaskiyar abin da ya faru
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata ya koka kan jita-jitar mutuwar Akpabio
Sanata Titus Zam ya bayyana irin wadannan rahotanni a matsayin masu hatsari da kuma illa ga shugabancin Najeriya, jaridar Daily Trust ta dauko labarin.
“Ina tayar da wannan batu ne saboda rahotannin kafafen sada zumunta da suka yi ikirarin cewa Shugaban Majalisar Dattawa ya rasu a wani asibiti da ke Landan."
“Wannan lamari ne mai matukar muhimmanci, mutum na uku mafi girma a Najeriya. Ya kamata a binciki irin wadannan rahotanni a kanka, a mutuncinka da ofishinka."
- Sanata Titus Zam
Ana yada jita-jitar mutuwar manyan mutane
Sanata Zam ya ce yaduwar labaran mutuwa na karya na zama al’ada, inda ya tuna cewa kwanan nan an yi makamancin wannan ikirari game da tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon.
“Ba kai kadai aka yada wannan mummunan labari a kanka ba; tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon, ma an ce ya rasu kwanakin baya. Wannan ba kyakkyawan labari ba ne game da shugabannin kasarmu."

Kara karanta wannan
Matawalle: Kungiya ta ba Tinubu shawarar abin da ya dace da karamin Ministan tsaro
“Idan aka dauki tsauraran matakai kan masu yada irin wadannan labaran karya game da shugabanninmu, hakan zai zama darasi ga duk wanda ke aikata wannan mummunan aiki mai hatsari ga shugabancin dimokuradiyyarmu da kasarmu.”
- Sanata Titus Zam
Sanata Zam ya kara da cewa ana iya gano wadanda ke da alhakin yada labaran ta hanyar bin diddiginsu.

Source: Facebook
Wane mataki majalisa ta dauka?
Da yake mayar da martani, Akpabio ya ce matsalar labaran karya ba ta tsaya kan ’yan siyasa kadai ba, yana mai cewa yada bayanan karya ya shafi fitattun mutane a bangarori daban-daban.
Daga bisani, shugaban majalisar dattawan ya bukaci ONSA da DSS da su gano tushen labaran karyar da masu yadawa, tare da daukar matakan da suka dace a kansu.
Batun rashin lafiyar shugaban majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa an ambato wasu majiyoyi na cewa Sanata Godswill Akpabio ya yanke jiki ya fadi saboda rashin lafiya.
Majiyoyin sun bayyana cewa an garzaya da shugaban majalisar dattawan zuwa wani asibiti a Landan sakamakon rashin lafiyarsa.
Sai dai, hadiminsa ya fito ya bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a cikin wadannan labaran da aka yada.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng