Babbar Magana: CBN Ya Soke Lasisin Bankuna 2, Sun Daina Aiki a Najeriya

Babbar Magana: CBN Ya Soke Lasisin Bankuna 2, Sun Daina Aiki a Najeriya

  • Bankin CBN ya bayyana cewa ba zai lamunci bankuna su jefa kudin da jama'a ke ajiyewa cikin garari ba, zai dauki matakin da ya dace
  • Babban bankin Najeriya ya sanar da soke lasisin wasu bankuna biyu na bangaren ba da rance da ajiyar kudi don mallakar gida a Najeriya
  • CBN ya ce bankunan da lamarin ya shafa sun gaza a bangarori da dama, ciki har da mafi karancin jarin aiki da doka ta kayyade

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babban bankin Najeriya (CBN) ya dauki mataki mai tsauri kan bankuna biyu da ke bangaren harkokin ajiyar kudi da bayar da rance don mallakar gida watau Mortgage.

Bankin CBN ya zargi wadannan bankuna da karya doka da saba ka'idojin harkokin kudi, wanda ya ce ba zai lamurci su ci gaba aikinsu ba a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan ganin bidiyon Bello Turji, APC ta hango dalilin alakanta Matawalle da 'yan bindiga

Gwamnan CBN.
Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso Hoto: @Centbank
Source: Getty Images

CBN ya soke lasisin bankuna 2

Leadership ta ce CBN ya soke lasisin bankin Aso Savings and Loans Plc da bankin Union Homes Savings and Loans Plc, a wani yunkuri na gyara da sake tsara bangaren bankunan mallakar gidaje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CBN ya sanar da wannan mataki ne ta cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, wadda Daraktar Sashen Hulɗa da Jama’a ta wucin gadi, Hakama Sidi Ali, ta sanya wa hannu.

A cewar CBN, ya ɗauki wannan mataki ne bisa ikon da doka ta ba shi a Sashe na 12 na Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kuɗi (BOFIA) ta 2020, da Sashe na 7.3 na Sabbin Ƙa’idojin Bankunan Jinginar Gida a Najeriya.

Wane laifi bankunan suka yi wa CBN?

CBN ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa bankunan da abin ya shafa sun karya wasu muhimman tanade-tanaden BOFIA 2020 da kuma ƙa’idojin bankunan Mortgage.

Kara karanta wannan

An kaddamar da shirin YouthCred, matasa za su iya samun Naira miliyan 5 a Najeriya

Daga cikin laifuffukan da aka gano akwai gazawar bankunan guda biyu na cika mafi ƙarancin adadin hannun jari da ya dace da irin lasisin da aka ba su.

Sanarwar ta ƙara da cewa kadarorin da bankunan ke da su ba su kai yadda za su iya biyan bashin da ke kansu ba, lamarin da ya jawo damuwa kan aminci da tsaron kuɗaɗen jama'a.

Haka kuma, CBN ya ce bankunan sun shiga matsanancin ƙarancin jari, inda ƙimar jarinsu ta faɗi ƙasa da mafi ƙarancin da dokar kula da bankuna ta tanada.

Wannan yanayi, a cewar bankin, ya rage musu damar gudanar da aiki cikin aminci da ɗorewa a tsarin kuɗin ƙasa.

CBN ya jaddada matsayarsa kan bankuna

Babban Bankin ya kuma zargi cibiyoyin da rashin bin wasu umarnin da ka’idojin da aka shimfiɗa musu a matsayin wani ɓangare na kulawar da ake yi musu daga bangaren masu sa ido.

“CBN na nan daram kan aikinsa na tabbatar da aminci a tsarin mu'amalar kuɗi,” in ji sanarwar.
Bankin CBN.
Hedkwatar babban bankin Najeriya (CBN) da ke Abuja Hoto: @CentBank
Source: Twitter

CBN ya ƙara da cewa zai ci gaba da ɗaukar duk matakan da suka dace domin kare martabar tsarin bankuna da kuma kare muradun masu ajiya da sauran masu ruwa da tsaki, cewar rahoton Bussiness day.'

Kara karanta wannan

'Ko $1bn aka ba ni, ba zan shiga sabgar ba': Malamin addini ya tsinewa siyasa

CBN ya canza tsarin cire kudi a banki

A wani rahoton, kun ji cewa bankin CBN ya sanar da cewa daga farkon watan Janairu, 2026, za a soke takaita adadin kudin da mutum ko kamfani zai iya ajiye wa a banki.

Haka kuma, an kara adadin kudin da za a iya cirewa a mako ga mutum ɗaya zuwa N500,000, sannan N5m ga kamfanoni.

CBN ya kuma soke tsarin da ya bai wa mutum damar cire N5m sau daya a wata da kuma N10m ga kamfanoni, wanda a baya ake bukatar samun izini na musamman kafin samun kari.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262