Mutane Sun Zo Wuya, Sun Kama 'Dan Bindiga Sun Yanke Masa Hukunci a tsakiyar Gari

Mutane Sun Zo Wuya, Sun Kama 'Dan Bindiga Sun Yanke Masa Hukunci a tsakiyar Gari

  • Mutanen gari sun yi kukan kura, sun tare yan bindigar da suka kai farmaki makwaftansu a yankin Bakura ta jihar Zamfara
  • Rahoto ya nuna cewa 'yan bindigar sun arce, amma mutane sun kama daya daga cikinsu kuma sun yi masa taron dangi
  • Wannan nasara da mutanen gari suka samu kan yan bindiga na zuwa a daidai lokacin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a wasu sassan Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - 'Yan bindiga sun gamu da fushin jama'ar gari yayin da suka kai farmaki kauyen Yargeda da ke Karamar Hukumar Bakura a Jihar Zamfara.

Rahotanni sun nuna cewa jama'a sun yi nasarar kama daya daga cikin 'yan bindigar da suka kai masu hari, kuma sun dauki mataki a kansa nan take.

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin Najeriya sun bi sawun 'yan bindiga, sun gano mutane 3 a jihar Kano

Jihar Zamfara.
Taswirar jihar Zamfa da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan al'amuran tsaro a Najeriya ya tabbatar da aukuwar lamarin a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce mutanen yankin da ke Karamar Hukumar Bakura a Jihar Zamfara sun kashe wanda ake zargin ɗan bindiga ne, bayan sun kama shi yayin wani hari da aka kai yankin.

Matasa sun tare 'yan bindiga a Zamfara

Ya bayyana cewa ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Yargeda a daren Juma’a, inda suka yi garkuwa da mutane uku.

A cewar rahoton, an kama wanda ake zargin ne yayin da shi da sauran ’yan bindigar ke ƙoƙarin wucewa da mutanen da suka sace ta cikin daji a kusa da ƙauyen Rini, inda wasu daga cikin mazauna yankin suka tare su.

Rahoton ya ce yayin da sauran ’yan bindigar suka tsere, ɗaya daga cikinsu bai samu damar guduwa ba, lamarin da ya sa jama’ar yankin suka kama shi.

Hukuncin da mutane suka yanke wa dan bindiga

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

An bayyana cewa mazauna ƙauyen sun ɗaure wanda ake zargin, suka hallaka shi, sannan suka rataye gawarsa a kan wani tankin ruwa da ke tsakiyar kauyen.

A ’yan kwanakin nan, hare-haren ’yan bindiga na ƙara yawaita a sassa daban-daban na ƙasar nan, musamman a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma.

A ranar 13 ga Disamba, wasu matafiya da ke bin hanyar Gurusu–Gwashi a Karamar Hukumar Bukkuyum suka taka wani bam (IED) da ake zargin ’yan bindiga ne suka dasa shi.

Gwamnan Dauda Lawal.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal a fadar gwamnatinsa da ke Gusau Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Wannan al'amari ya tada hankulan mazauna yankin amma jami'an tsaro sun bincike gaba daya yankin domin tabbatar da babu wani bam din, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Wannan mataki da jama'ar gari suka dauka kan 'dan bindigan da suka kama a yankin Bakura ya nuna yadda mutane suka fusata da matsalolin tsaron da ke addabarsu.

Yan bindiga sun kakabawa mutane haraji

A wani rahoton, kun ji cewa mazauna kauyukan da ke cikin Karamar Hukumar Bungudu a Jihar Zamfara sun sake tashi da wata matsala daga yan bindiga.

Rahoto ya nuna ’yan bindiga sun ƙara matsa lamba tare da kakaba haraji mai nauyi kan manoma da ke son girbe amfanin bana a yankin.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa dan sandan Najeriya hukuncin kisa, za a rataye shi har lahira

An ce wadanda abin ya shafa sun ce a yanzu ba a bari manoma su kusanci gonakinsu sai sun biya kudin da ’yan bindigan suka ce dole sai an biya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262