Elon Musk Ya Zama Mutumin Farko a Duniya da Dukiya Ta Haura Dala Biliyan 600

Elon Musk Ya Zama Mutumin Farko a Duniya da Dukiya Ta Haura Dala Biliyan 600

  • Fitaccen attajiri a duniya, Elon Musk ya taka karin matsayi inda ya zama mai kudin da dukiyarsa ta haura matakin da ba a taba ji ba
  • Wannan gagarumin mataki ya kara kusantar da shi zama mutumin farko a duniya da dukiyarsa za ta kai Dala tiriliyan daya a duniya
  • A farkon wannan wata, kamfanin harba rokan shi nasa, ya kaddamar da wani shirin sayen hannun jari da ya ƙimanta kamfanin a kan $800bn

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

South Africa – Fitaccen attajiri, Elon Musk ya sake taka wani gagarumin mataki da ke kara kusantar da shi zama mutumin farko a duniya da dukiyarsa za ta kai $1trn.

A farkon wannan wata, kamfanin harba roka nasa, SpaceX, ya kaddamar da wani shirin sayen hannun jari da ya ƙimanta kamfanin a kan Dala biliyan 800, daga Dala biliyan 400 da aka ƙimanta shi a watan Agusta.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari ya yarda matarsa, Aisha za ta kashe shi a Aso Rock Villa

Arzikin Elon Musk ya haura Dala tiriliyan daya
Elon Musk, fitaccen mai arziki a duniya Hoto: @realDonaldTrump
Source: Getty Images

Mujallar Forbes ta wallafa cewa kamar wannan sabon ƙima ya ƙara wa dukiyar Musk Dala biliyan 168, duba da cewa yana da kusan kashi 42 cikin 100 na SpaceX.

Arzikin Elon Musk ya karu

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kai jimillar dukiyarsa zuwa kimanin Dala biliyan 677 zuwa ranar Litinin da rana, lamarin da ya sa ya zama mutumin farko a tarihin duniya da dukiyarsa ta haura Dala biliyan 600.

Wannan tayin sayen hannun jari na zuwa ne a lokacin da SpaceX ke shirin shiga kasuwar hannun jari ta duniya (IPO) a shekarar 2026, wanda ake hasashen zai iya kai ƙimar kamfanin zuwa kusan Dala tiriliyan 1.5.

Elon Musk ya samu tagomashi daga kamfanin Tesla
Fitaccen attajiri a duniya, Elon Musk Hoto: Elon Musk
Source: Getty Images

Hannun jarinsa na kashi 12 cikin 100 a Tesla kuwa na da kimar Dala biliyan 197, ba tare da haɗa wasu zaɓaɓɓun hannun jari daga kyauta da ya samu a aikinsa a shugabanci a 2018 ba da kotu a Delaware ta soke.

Kara karanta wannan

'Ko $1bn aka ba ni, ba zan shiga sabgar ba': Malamin addini ya tsinewa siyasa

Bayan soke kimar hannun jarin a Janairun 2024, Forbes ta rage ƙimar waɗannan zaɓaɓɓun hannun jari da kashi 50, zuwa Dala biliyan 69, har sai an yanke hukunci kan ƙarar da Musk ke yi.

Elon Musk ya samu tagomashi

A watan Nuwamba, masu hannun jarin Tesla sun amince da wani kunshin albashi mai tsoka da zai iya bai wa Musk har zuwa Dala tiriliyan 1 a hannun jari.

Baya ga haka, kamfanin xAI Holdings na Musk na tattaunawa kan sabon ɗaukar jari a ƙimar Dala biliyan 230, fiye da ninki biyu na ƙimar da ya ambata lokacin da ya kafa kamfanin.

A cikin shekaru biyar da suka gabata, dukiyar Musk ta tashi daga Dala biliyan 24.6 a 2020 zuwa sama da Dala biliyan 600 a yau.

Yanzu haka, yana da gibin kusan Dala biliyan 425 tsakaninsa da na biyu mafi arziki, Larry Page. Kuma kasancewar ya rage masa Dala biliyan 23 kacal kafin ya kai Dala biliyan 700.

Musk ya zarce raini a sahun attajirai

A baya, mun wallafa cewa shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk, wanda haifaffen Afrika ta Kudu ne amma ke zama a Amurka, ya zarce kowa wajen dukiya, domin dukiyarsa ta kara habaka yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Dangote ya rubuta wasiyya, za a cire wani kaso mai tsoka a dukiyarsa idan ya rasu

Rahotanni sun tabbatar da cewa dukiyarsa ta kai Dala biliyan 447, kamar yadda Bloomberg Billionaires Index ta nuna, wannan na nufin kudin ya kai kusan Naira tiriliyan 690, kuma tana ci gaba da karuwa

Wannan ya sa ya ba Jeff Bezos, wanda ke kan kamfanin Amazon, gibin Dala biliyan 190 a sahun attajirai na duniya. Dukiyar Musk ta hada da hannun jarinsa na kamfanin Tesla, wanda ya ci gaba da habaka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng