Jirgin Ruwan Najeriya da Wasu Kasashe da Suka Fada Tarkon Amurka a 2025
Bayan dawowar Donald Trump mulki a shekarar 2025, dakarun sojojin Amurka sun kwace jiragen ruwa da tankokin mai daga wasu kasashe ciki har da Najeriya.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Amurka ta tsananta sintiri game da tsaro musamman a cikin teku kamar yadda jami'an gwamnatin kasar suka tabbatar.
Amurka ta kai samame a cikin ruwa tare da kwace tankokin mai da wasu kayayyaki da suka fito daga wasu kasashe zuwa wasu a fadin duniya.

Source: Getty Images
A wannan rahoton, mun hada muku rahoto na musamman game da jiragen ruwa da Amurka ta kwace wa kaya a 2025.
1. Amurka ta kwace tankar man Najeriya
Rahoto ya nuna cewa an kwace wata tsohuwar tankar mai da ya kai kimanin shekaru 20 tana zirga-zirga a ruwan tekun Yammacin Afirka da Kudancin Amurka.
Duk da cewa ana alakanta tankar da kamfanin Thomarose Global Ventures na Legas, bayanan rajistar kasa-da-kasa sun bayyana Triton Navigation Corp da ke Marshall a matsayin sahihin mamallakinta.
Hukumomin kasar Guyana sun tabbatar da cewa tankar ta yi amfani da tutar kasarsu ba tare da izini ba, lamarin da suka bayyana a matsayin karya da yaudara.
Vanguard ta rahoto cewa sun kara da cewa sauya tutar jirgi dabara ce da wasu masu laifuffukan teku ke amfani da ita domin kauce wa doka ko rikitar da jami’an tsaro.

Source: Getty Images
Jami’an tsaron Amurka sun ce sun kwace tankar ne a doron doka bayan gano yiwuwar alakanta ta da satar mai, fasa-kwauri da kuma safarar miyagun kwayoyi.
Masana daga Najeriya sun bukaci gudanar da bincike domin tabbatar da ko jirgin ruwan ya tashi daga kasar ne ba tare da an tantance shi ba.
2. Amurka ta tsare jirgin China zuwa Iran
New York Times ta bayyana cewa dakarun Amurka sun shiga wani jirgin dakon kaya da ke tafiya daga China zuwa Iran, sun kwashi wasu kayayyaki.
Wani rahoto ya ce wata rundunar ayyuka na musamman ta sojojin Amurka da ke Tekun Indiya ce ta kai samame kan jirgin.

Source: Getty Images
Legit Hausa ta rahoto cewa Amurka ta kwace kayayyakin da ke da alaƙa da harkokin soji, kamar yadda jami’an kasar suka bayyana.
Wani jami’i ya ce kayan da ke cikin jirgin sun ƙunshi sassa da za su iya zama masu amfani ga makaman gargajiya na Iran, inda ya ƙara da cewa an lalata kayan gaba ɗaya.
3. Amurka ta kwace tankar man Venezuela
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka ta kwace wata tankar mai da aka sanya mata takunkumi a gabar tekun Venezuela.
Rahoton Reuters ya nuna cewa Trump ya ce:
“Mun kwace wata tankar mai a gabar tekun Venezuela, babbar tankar mai ce ƙwarai.”
Lokacin da aka tambaye shi abin da zai faru da man da ke cikin tankar, Trump ya amsa da cewa:
“Za mu riƙe tankar ne, a gani na.”
A martaninta, gwamnatin Venezuela ta zargi Amurka da abin da ta kira “sata a fili,” inda ta bayyana kwace tankar a matsayin “aikin fashin teku na ƙasa-da-ƙasa.”

Source: Twitter
An ce wannan karo na farko da Amurka ta kwace jigilar man Venezuela tun bayan kakaba takunkuman da aka fara aiwatarwa a shekarar 2019.
Amurka ta gargadi 'yan Najeriya kan biza
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta gargadi 'yan Najeriya da su rika kiyaye dokokinta wajen neman biza.
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ne ya yi gargadin, inda ya ce ba zai lamunci amfani takardun bogi wajen neman shiga kasar ba.
Gwamnatin Amurka ta ce za ta dauki matakai masu tsauri kan duk wanda aka kama da laifi, ciki har da hana shi shiga kasar har abada.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


