Rikici Ya Kaure a tsakanin Yan Kasuwa, Ana Gasar Rangwamen Farashin Fetur
- Rage farashin mai a matatar attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya fara jawo wa yan kasuwa da suke da mai mai tsada matsala
- Rahotanni sun tabbatar da cewa masu shigo da mai, mazu rumbunan ajiya da yan kasuwar mai sun fara kokawa game da saukar farashin
- Ana hasashen matatar Dangote za ta rasa kusan N91bn a wata guda saboda ragin, duk da cewa lamarin ya yi wa talakawa dadi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Kasuwar man fetur a ɓangaren ta rikice yayin da ake gwabzawa a kan farashi, bayan Matatar Dangote ta rage farashin mai a Najeriya.
Wannan mataki ya haifar da asara mai yawa ga masu shigo da mai, masu rumbunan ajiya da kuma ‘yan kasuwar man fetur, duk da cewa matatar Dangote ma na asarar kudi.

Source: Facebook
Binciken Jaridar Punch ya nuna cewa cewa masu shigo da mai na fuskantar yiwuwar asarar kusan N102.48bn a kowane wata, sakamakon rage farashin daga N828 zuwa N699 kan kowace lita.
Matatar Dangote za ta yi asara
Rahoton ya kara da cewa ana hasashen matatar Dangote za ta rasa kusan N91bn a wata guda, wanda ke nuna tsananin gasar da ke sake fasalin kasuwar man fetur a ƙasa.
Duk da cewa ‘yan Najeriya da dama sun yi maraba da rage farashin, musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti, ‘yan kasuwar gidajen mai sun ce suna fuskantar mummunar asara.
Hakan ya faru ne saboda dole su sayar da tsohon man da suka saya a farashi mai tsada ƙasa da kuɗin da suka kashe.

Source: Getty Images
Matatar Dangote ta sanar da rage farashin ne da N129 a kowace lita, tare da tabbatar da cewa akwai wadataccen mai domin guje wa layuka a gidajen mai.
Haka kuma, kamfanin ya ba ‘yan kasuwa damar karɓar kaya bashi na kwanaki 10, inda sabon farashin ya fara aiki daga 12 ga Disamba.
Shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya jaddada cewa dole ne a sayar da fetur a N739 a kowace lita a faɗin ƙasa.
Masu shigo da mai sun shiga matsala
Don ci gaba da yin gogayya, masu shigo da mai da masu rumbunan ajiya sun rage farashinsu, lamarin da ya haddasa asara a dukkan sassan sarkar rarraba mai.
Rahotanni sun nuna cewa a Legas, farashin mai a rumbuna masu zaman kansu ya faɗi da kusan kashi 14 cikin 100 cikin ‘yan kwanaki.
Hukumar NMDPRA ta ce Nijeriya na cin kimanin lita miliyan 50 na fetur a kullum, wato lita biliyan 1.5 a wata. Dangote na samar da kusan lita miliyan 705.6 a wata.
Masu shigo da mai ke samar da sauran lita miliyan 794.4. Da yake magana, kakakin IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce masu shigo da mai, musamman waɗanda jiragensu ke kan ruwa, na cikin mawuyacin hali.
Ya ce gidajen mai ma za su iya rasa sama da N80bn saboda sayar da man da suka saya a farashi mai tsada ƙasa da kuɗinsa.
Dangote ya yi magana game da Trump
A wani labarin, kun ji cewa Aliko Dangote, attajirin Afrika kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya karyata rade-radin da ke yawo cewa gwamnatin Amurka na nuna rashin jin dadi game da ayyukan matatar mansa.
Dangote ya ce wadannan ikirari ba su da tushe balle makama, yana mai jaddada cewa akasin haka ne ke faruwa domin Donald Trump bai saka ido ko takaicin ci gaban da ake samu a Najeriya ba.
A cewarsa, Shugaba Donald Trump na cikin mutanen da suka fi nuna farin ciki da yadda matatar Dangote ke aiki, musamman idan aka yi la’akari da girman alakar kasuwanci da ke tsakanin Najeriya da Amurka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


